‘Yan bindiga sun kashe mutum 7, sun sace 26 a Neja

0
114

‘Yan bindiga sun kashe mutum bakwai tare da sace wasu 26 a karamar hukumar Mashegu da ke Jihar Neja.

A cewar shugaban karamar hukumar, Umar Jibrin Igede, wanda ya tabbatar da harin da ‘yan bindiga suka kai yankuna bakwai a Minna a ranar Lahadi, ya bayyana cewa, hare-haren sun sa daruruwan mazauna yankin tserewa daga gidajensu.

Igede ya kuma bayyana cewa ‘yan bindigar sun kashe daruruwan mazauna yankin tsakanin watan Janairu zuwa Maris 2023.

“Tuni ‘yan bindiga suka sa mutanenmu barin gidajensu saboda hare-hare.

“A cikin makonni biyun da suka gabata, ‘yan ta’adda sun kai hari a Kulho, Sahon Rami, da Tashan Hajiya da sauran yankuna.

“Yawancin mazauna kauyukan da lamarin ya shafa sun bar gidajensu zuwa sansanin ‘yan gudun hijira da ke Kontagora da sauran wurare domin kare lafiyarsu.”

Shugaban ya yi kira ga gwamnatin jihar da sauran jami’an tsaro da abin ya shafa da su kawo musu dauki domin kawo karshen hare-haren ta’addanci a karamar hukumar.

“Hare-haren da ake kai wa jama’a na na haifar da babbar barazana ga tsaro ga mazauna kauyukan.”

Jin ta bakin kakakin ‘yan sandan Jihar, DSP Wasiu Abiodun, ya ci tura.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here