‘Yan jahohin Arewa ke kan gaba wajen yawan mabarata a Abuja

0
111

Hukumar Babban Birnin Tarayya Abuja a ranar Lahadi ta mayar da wasu mabarata da masu gararamba a kan tituna kimanin 217 zuwa jihohinsu na asali.

Daraktan Sashen Kula da walwalar Jama’a da ci Gaba na hukumar, Alhaji Sani Amar Rabe, ne ya shaida wa Kamfanin daillancin Labarai na Najeriya (NAN) hakan a cibiyar koyar da sana’o’i da ke Bwari, bayan an kwashe mutanen zuwa jihohin nasu.

Ya ce daukar matakin ya biyo bayan umarnin da Minista a Ma’aikatar Babban Birnin, Ramatu Aliyu da Babban Sakataren Ma’aikatar suka bayar na tsaftace birnin daga mabarata.

Alhaji Sani ya ce alhakin sashen ne ya tabbatar da cewa dukkan mutanen da aka kama din an mayar da su inda suka fito.

“Mun zo nan ne domin mu mayar da mabarata da masu yawon banza da sauran bata-gari da aka tabbatar zamansu ba shi da amfani. Mun bincika lafiyarsu, kuma wasu daga cikinsu ma har sun nuna sha’awar suna son su koyi sana’a.

“Yau mutanen da za mu mayar ba su da yawa; su 217 ne kacal, kuma galibinsu za mu mayar da su ne jihohin da suka fito na Katsina da Kaduna, Neja da Jigawa da Kano da Zamfara da Sakkwato da kuma Kebbi.

“Kazalika, wannan karon akwai kuma wadanda suka fito daga Jihohin Abiya da Imo da Delta.”

Daraktan ya kuma ce tuni Ministar ta fara tattaunawa da Gwamnonin Jihohin da mutanen suka fito, ta hanyar ofisohin tuntubarsu da ke Abuja, domin duba yadda za a magance ci gaba da kwararowar mutanensu a nan gaba.

Daga nan sai ya shawarci masu hannu da shuni a birnin da su daina bayar da sadaka ga mabaratan saboda yin hakan a cewarsa na dada karfafa musu gwiwa su ci gaba da yi. (NAN)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here