Ƙungiyar ƴan mata masu fama da kaɗaici na ƙara samun karɓuwa

0
109

Kusan mata 20,000 ne da ke zaune a London, suka shiga ƙungiyar ƴan mata masu fama da kaɗaici tun bayan kawo ƙarshen takunkuman da aka sanya lokacin annobar korona.

Holly Cooke ta kafa kungiyar ne a shafin Facebook cikin 2018 bayan komawa birnin London daga Stoke-on-Trent.

Ta ce ƙungiyar na da mambobi 10,000 a farkon shekara ta 2022, inda kuma take ci gaba da karɓuwa a tsawon shekara ɗaya da ya wuce zuwa kusan mutum 31, 000.

“Mutane da yawa sun dawo birnin London, kuma suna son shiga wannan ƙungiya,” in ji Cooke.

“London na da girman gaske, tana da wurare na zaman kaɗaici.”

Matashiyar ‘yar shekara 26 da ke zaune a arewa maso gabashin London, ta koma can ne da mutanen gidansu da kuma ƴan’uwanta lokacin da ta fara isa birnin, inda ta sha fama kafin samun ƴan mata masu shekaru irinta.

“Na duba shafin matambayi ba ya ɓata na Google a kan yadda mutum zai samu ƙawaye a London,” in ji ta.

Mis Cooke ta ce haɗuwa da mutane a shafukan sada zumunta kamar na Bumble BFF “ya zama abin tsoro”.

“Na tuna cewa ‘Shin yaya zan yi, idan zan samu ƙawaye biyu ko uku ko kuma huɗu duk a lokaci ɗaya?’, in ji Cooke.

Ganin irin shakkun da cike da zuciyarta na irin ƙawayen da za ta haɗu da su, shi ya sanya ta ƙirƙiro shafin Facebook ɗin ta.

“Zaman kaɗaici na da matuƙar wahala,” in ji ta. “Ba ya la’akari da wanne sashe mutum yake rayuwa.

“Mutane na fama da zaman kaɗaici ta hanyoyi da dama. London na saurin canzawa. Wasu sun dawo nan ne yanzu; wasu kuma suna nan ne muddin rayuwarsu.”

Ita, da wasu ‘yan sa-kai biyu suna shirya bukukuwa huɗu zuwa shida duk wata, waɗanda suka haɗar da yin wasanni, sannan a yi ciye-ciye da kuma sauran ‘yan kayan taɓa-ka-lashe.

Kowacce mamba ta kungiyar tana da damar halartar bukukuwan, amma da yawa sanannun ƴan mata ne.

Wani rahoto da aka wallafa a watan Disamba, ya ce duk ɗaya cikin ƴan London 12, suna fama da zaman kaɗaici.

Wata cibiya mai taken Gangami don Kawo Ƙarshen Zaman Kaɗaici ce ta gudanar da binciken da haɗin gwiwar wasu ƙungiyoyi a London.

Binciken ya gano cewa annobar korona ta ƙara jefa mutane cikin kaɗaici, inda aka gano cewa mutum 700,000 na fama da rayuwar kaɗaici a yawan lokuta.

Binciken ya ce kashi 12 na ƴan mata sun fuskanci matsanancin kaɗaici, inda mutane ke yin sauye-sauyen rayuwa ko kuma zuwa London.

Har ila yau, an gano cewa talauci da son zuciya da kuma nakasa na iya ƙara jefa mutum cikin hatsarin nesanta kai da sauran jama’a.

Mis Cooke ta ce ƙungiyarta ta samar da “ingantacceen muhalli” don mutane su riƙa haɗuwa suna mu’amala.

“Ana neman izinin haɗuwa cikin minti biyar,” in ji ta. “Mun sayar da izinin haɗuwarmu ta farko bayan cutar korona a cikin minti biyu.

“Tafiyar ta kasance, ba mai sauki ba, na fara ne saboda kawai ina son yin ƙawaye.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here