Kalaman Peter Obi sun yamutsa hazo a siyasar Najeriya

0
92
A Najeriya, cacar-baki ta kaure tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar da na jam’iyyar Labour mai adawa.

Lamarin na zuwa ne, tun bayan jin wata tattaunawar wayar salula tsakanin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi da Bishop David Oyedepo, wani babban limamin Kirista na majami’ar Living Faith Church.

A ƙarshen mako ne, wata jaridar intanet mai suna People Gazette ta wallafa wannan murya da aka kwarmata, tsakanin Peter Obi da babban limamin Kiristan, Bishop David Oyedepo.

Wannan ya janyo ce-ce-ku-ce da zazzafar muhawara a shafukan sada zumunta a ƙasar.

Musamman ma yadda aka ji ɗan takarar yana roƙon malamin ya taimaka wajen nema masa goyon bayan mabiya addinin kirista da ke shiyyar kudu maso yammacin Najeriya da kuma shiyyar arewa ta tsakiyar ƙasar.

Ya dai alaƙanta siyasar da takararsa, tamkar wata fafutukar yaƙi na addini, har ma ya tattabar wa limamin Kiristan da cewa ba za su yi da-na-sanin goya masa baya ba.

`Yan jam`iyyar APC mai mulkin Najeriya sun yi ca a kan dan takarar shugaban kasar suna cewa asirin sa ne ya tonu, kuma zargin da suke yi cewa siyasar sa ta addini da kabilanci ce ya tabbata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here