Mahara sun kashe mutum 10 sun kona gidaje 50 a Kogi

0
117

Yan bindiga sun hallaka mutum 10 tare da kona gidaje sama da 50 a yankin Aloko-Oganenigwu da ke Karamar Hukumar Dekina ta Jihar Kogi.

Wani mazaunin yankin, David Abimaje ya ce, “Maharan da ake zargi sun fi mutum 100 da suka shigo yankin ne dauke da bindigogi da jarkokin fetur suna harbin mutane tare da banka wa gidaje sama da 50 wuta.”

Da yake bayani a lokacin da mataimakin gwamnan jihar, Edward Onoja ya kai musu ziyarar jaje, ya ce bayan harin na ranar Lahadi, an tsinci gawarwaki 10 a unguwannin Aloko-Oganenigu da unguwar Edede da kuma Ojuole.

Ya ce maharan sun nufi yankunan Ojoapata da Ojole da kuma Ubaobu kafin amam aka tura sojoji cikin gaggawa suka dakile su.

Gwamna Yahaya Bello, ya umarci hukumomin tsaron jihar su yi bincike kan musabbain harin da nufin gano wadanda suka kai shi, domin su fuskanci hukunci.

Ya ce, “Duk da cewa ba a saba kai irin wannan bari ba, amma a 2018 an kai wa wani kauye da ke yankin  hari; saboda haka wannan ne zai zama na karshe domin gwamnati ba za ta zuba ido ba ana kashe mutane haka kawai ba; sai mun hukunta masu aikatawa.”

Gwamnan ya jinjina wa jami’an tsaro bisa matakan gaggawa da suka dauka wajen hana yaduwar matsalar da kuma barnar da ta haifar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here