Ba za mu saka addini a kidayar Najeriya ta 2023 ba — NPC

0
114

Hukumar Kidaya ta Nijeriya, NPC ta musanta wani labari da ake yadawa cewa za a yi tambayoyi game da addini a lokacin kidayar da za a gudanar a watan Mayu.

Ana ta yada wani sakon murya a manhajar Whatsapp inda ake kira ga Musulmai da su sani cewa za a tambaye su game da addininsu a matsayin wata hanya ta rage musu yawa a kidayar da ke tafe.

Sai dai a sanarwar da daraktan watsa labarai na hukumar NPC Isiaka Yahaya ya fitar, ya ce bidiyon na bogi ne kuma ba su da wani shiri mai kama a lokacin gudanar da kidaya.

Ya tabbatar da cewa hukumar ta kidaya ba za ta yi wata tambaya da ke da alaka da addini ba.

“An dauki matakin cire batun addini da kabila daga takardar kidayar ne domin irin tsaurin da wadannan batutuwa ke da shi a Nijeriya da kuma kare kidayar daga ce-ce-ku-cen da ba shi da amfani,” in ji hukumar.

Haka kuma hukumar ta ce ta bi diddigi ta gano cewa an soma aikawa da wannan sakon ne a manhajar Whatsapp a lokacin kidayar da aka yi a Ghana a 2021.

Ta kuma ce an soma yada wannan sakon a Nijeriya a lokacin da aka yi gwajin kidaya a watan Yulin 2022.

An soma kidayar jama’a bayan samun ‘yancin kan Nijeriya ne a 1962 inda aka kididdige cewa jama’ar kasar sun kai miliyan 45.5.

Kidaya ta karshe da aka yi a kasar an yi ta ne a 2006 inda aka kididdige cewa akwai sama da mutum miliyan 140 a kasar, sa’annan a 2019 kuma hukumar ta yi hasashen cewa jama’ar kasar sun haura mutum miliyan 200.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here