Tasirin kudaden da shugaba Buhari ya bai wa jami’o’in Najeriya za su yi

0
143

A makon jiya ne Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya ya sanar da bai wa kowace jami’ar gwamnati a kasar naira biliyan daya da miliyan 154, a wani mataki na tallafa wa makarantun na shekarar 2023.

Wadannan kudade na cikin naira biliyan 320 da milyan 345 da Shugaba Buhari ya amince a bai wa jami’o’i da kwalejojin ilimi na kasar, in ji shugaban Asusun Raya Karatun Jami’o’i da Kwalejojin Ilimi (TETFUND), Sonny Echono.

Mista Echono ya ce kowace Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta sami kusan naira miliyan 700, yayin da kowace Kwalejin Ilimi za ta sami naira miliyan 800,862,602.

“Wannan shi ne kudi mafi yawa da aka taba bai wa kowacce daga cikin makarantun tun da aka kafa TETFUND,” in ji Echono.

Ya ce tun lokacin da aka kirkiro asusun TETFUND a shekarar 1993 zuwa shekarar 2014 asusun ya bai wa jami’o’i da kwalejoji naira tiriliyan 1.249.

Amma tsakanin shekarar 2014 zuwa shekara 2023 asusun na TETFUND ya raba naira tiriliyan 1.702 ga jam’i’o’i da kwalejoji.

Shin yaya masana ke ganin wannan mataki? Ta yaya kudaden za su taimaka wajen inganta tsarin karatun gaba da sakandare a kasar?

Shugaban TETFUND yana ganin wannan gagarumar nasara ce wadda ba ta rasa nasaba da damar da gwamnatin Shugaban Buhari ta bayar don asusun ya “kara harajin ilimi daga kashi 2.0 cikin 100 zuwa kashi 2.5 cikin 100 a shekarar 2021.”

Sai dai ba kowa yake ganin wannan a matsayin gagarumar nasara ba. Mataimakin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Nijeriya, Dr Chris Piwuna, yana ganin kudaden TETFUND da aka raba din sun yi kadan idan aka yi la’akari da yawan makarantun kasar.

“Ma’aikatar ilimi tana zuwa asusun (TETFUND) ba bisa doka ba don ta ba da kudin fara aiki ga sabbin makarantu, lamarin da ke kara rage yawan kudaden da makarantu za su samu,” in ji Dr Piwuna a hirarsa da TRT Afrika.

Ya kara da cewa tattalin arzikin kasar ya shiga mawuyacin hali kuma darajar kudin kasar, naira ta fadi.

“Wannan ya sa kudin gina dakin lakca da sauran ababen more rayuwa a makarantu suka kara tsada sosai,” in ji Dr Piwuna.

Ya ce kudin horas da malamai karatun digiri na biyu da na uku ya kusa fin karfin makarantun. “Abu kadan za mu iya yi da biliyan 320. Gaya mini abin da naira miliyan 600 za ta yi wa Kwalejin Kimiyya da Fasaha,” a cewarsa.

Asusun TETFUND yana bai wa makarantu kudaden ne don su samar da muhimman ababen more rayuwa da za su inganta tsarin koyarwa da horas da malamai da kuma tabbatar da ingancin aikin makarantun.

Sauran kudaden

 

Da yake magana a kan kudin da asusun TETFUND ta raba wa makarantun, Shugaban Kuniyra Malaman Jami’ar Nijeriyar, Emmanuel Osodeke, ya ce ya kamata a sake raba kudin.

“Kudin ci gaba ne mai kyau, wannan ya kasance daya daga cikin abubuwan da muka yi gwagwarmaya a kai a shekarar 1994.

“Gwagwarmayarmu ce, amma akwai abubuwan da ya kamata a warware,” a cewar Osodeke a lokacin da yake magana da gidan talibijin na Channels na kasar.

“Idan ka dubi kasafin kimanin naira biliyan 1.2 da aka bai wa jami’o’i da sauran su, za ka ga jumullar kudaden da aka bai wa jami’o’i da Kwalejojin Kimiyya da Fasaha da kuma Kwalejojin Ilimi sun kasance naira biliyan 186 daga cikin biliyan 320,” in ji shi.

Ya ce kudin zai rage naira biliyan 132 wanda ya kasance kashi 41 cikin 100 na kudin.

“Ina ganin ya kamata a sake raba kudin ta yadda zai kasance kashi 90 cikin 100 na abin da aka ce a raba wa jami’o’i da kwalejojin kimiyya da fasaha, ba wai kawai a jiye kudin ga harkar gudanarwa ba ko wani abu,” a cewar Osodeke.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here