Burkina Faso ta fito da ‘dukkan sojinta’ don yakar ‘yan bindiga

0
150

Gwamnatin Soji ta Burkina Faso ta kaddamar da wani shiri na fito da duka sojojinta don bai wa kasar dukkan abin da ake bukata a yaki da ‘yan bindiga da ke kai hare-hare tun farkon shekarar nan.

Manufar hakan ita ce a samar da “wani yanayi na doka kan dukkan matakan da za a dauka” don yaki da masu tayar da kayar baya, kamar yadda wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar a ranar Alhamis ta ce.

Kyaftin Ibrahim Traore, shugaban kasar gwamnatin rikon kwarya ta Burkina Faso wanda ya ya yi juyin mulki na baya-bayan nan ranar 30 ga watan Satumba, ya dauki aniyar kwato kashi 40 cikin 100 na yankin kasar, wanda ke karkashin ikon mayakan sa kan da ke da alaka da kungiyoyin Al Qaeda da Daesh.

“Yanayi da zaman lafiyar kasar nan ya danganta da irin kokarin da ‘ya’yanta ke yi na nemo mafita, a yanayin da ake ciki na matsalar rashin tsaro,” kamar yadda Ministan Tsaro Kanal Manjo Kassoum Coulibaly ya fada a wata sanarwa.

Ba a bayar da cikakken bayanin shirin ba, duk da cewa wata majiyar tsaro ta shaida wa AFP cewa shirin zai hada da “ayyana dokar ta-baci a yankunan da lamarin ya shafa.”

Kazalika hukumomi sun fitar da “jerin shawarwari” da suka bai wa shugaban kasa “damar ya kwace kadarorin mutane da kayayyaki da ababen more rayuwa da kuma takaita ‘yancin fadin albarkacin baki”.

Daukar sababbin sojoji aiki

Tuni gwamnatin ta sanar da shirin daukar karin sojoji 5,000 a watan Fabrairu, don yakar masu tayar da kayar baya da suka addabi kasar tun 2015.

A makon jiya, fararen hula 44 “kungiyoyin ‘yan ta’adda” suka kashe a kauyuka biyu da ke arewa maso gabashin Burkina Faso, a kusa da kan iyakar Nijar.

Shi ne hari mafi muni da aka kai kan fararen hula tun bayan da Traore ya hau mulkin kasar a watan Satumban bara, bayan da aka kashe soja 51 a watan Fabrairu a wani hari da aka kai Deou, a yankin arewa mai nisa na kasar.

A ranar Talata ne Ministan Tsaro ya yi wani kira ga sojoji masu ci da wadanda suka yi ritaya da su bayar da kakinsu da ba sa amfani da su ga sojoji mayaka.

Tun a shekarar 2012 ne rikici ya fara a yankin daga Mali, bayan da masu ta da kayar baya suka sace wani dan awaren Tuareg.

Tun daga lokacin rikicin ya yadu a makwabtan Malin, Burkina Faso da Nijar inda yake zama barazana ga sauran kasashe da ke kusa da teku.

Rikicin Burkina Faso ya yi sanadin mutuwar mutum 10,000 a cikin shekara bakwai da suka wuce, a cewar wasu kungiyoyin ba da agaji masu zaman kasu, ya kuma raba mutum miliyan biyu da muhallansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here