Abin da ‘yan Najeriya ke cewa kan korar ‘yan sandan da ke kare Rarara daga aiki

0
174

‘Yan Najeriya musamman wadanda ke amfani da soshiyal midiya suna ta yin tsokaci game da matakin da rundunar ‘yan sandan kasar ta dauka na korar wasu jami’anta da ke kare lafiyar fitaccen mawakin nan Dauda Kahutu Rarara.

A ranar Alhamis ne rundunar ‘yan sandan kasar ta sanar da korar ‘yan sanda uku bisa samunsu da laifi na “amfani da bindiga ba bisa ka’ida ba da wuce gona da iri da rashin da’a da kuma bata harsasai”.

‘Yan sandan da aka kora su ne Sufeto Dahiru Shuaibu da Sajent Abdullahi Badamasi da kuma Sajent Isah Danladi.

A makon jiya ne wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta ya nuna ‘yan sandan suna harba bindiga a iska don hana mutane matsawa kusa da mawakin yayin da yake kokarin shiga motarsa.

An kama ‘yan sandan da ke bai wa Rarara kariya

Rarara ya je kauyensu Kahutu ne domin yin ziyara, kuma a wata hira ya ce ‘yan sandan sun yi harbi ne domin kada bata-gari su kai masa hari.

Sai dai a wancan lokacin, rundunar ‘yan sandan kasar ta yi tir da “rashin kwarewa da rashin ɗa’a da ‘yan sandan suka nuna inda suke harba bindiga domin kuranta mawakin na Kano.

Rarara shahararren mawakin siyasa ne da yake goyon bayan jam’iyyar APC mai mulki a Nijeriya.

Korar ‘yan sandan ta jawo zazzafar muhawara inda mutane suka rika bayyana ra’ayoyinsu.

“Matakin ya dace”

Wani mai amfani da Twitter, Dr Victorsobe, ya ce yana ganin korar da aka musu ta yi daidai don hakan zai zama izina ga wasu.

Ya ce: “ Wannan ne mataki na farko na tsaftace rundunar ‘yan sandan Nijeriya. Da zaran jami’ai sun san ko wani laifi suka yi a bakin aikinsu ne, za su yi taka-tsantsan.”

Shi ma Sulaiman Muhammad Bauchi maraba ya yi da korar da aka musu a sakon da ya wallafa a shafin Facebook na TRT Afrika Hausa.

“Jinjina ga rundunar ‘yan sandan Nijeriya da wannan namijin kokarin, “ a cewarsa.

Zakariya Aliyu Gwaram ma yana ganin korar ta yi daidai, kamar yadda ya wallafa a shafin Facebook na TRT Afrika Hausa.

“Akwai ababen bajinta da hukumar ‘yan sandan Nijeriya ke yi don inganta ayyukansu. Wannan ma shaida ce. Allah Ya sa wannan ya zama darasi ga wadanda aikinsu ke hannunsu,” in ji shi.

Shi ma Habibu Abdullahi Habibu yana da irin wannan ra’ayin.

“Wannan gaskiya ya yi daidai ko dan jan kunne ga masu shirin yin hakan nan gaba,” kamar yadda ya wallafa a shafin TRT Afrika Hausa na Facebook

“Ya yi tsauri”

Hafiz Abubakar Nagode yana ganin hukuncin da rundunar ‘yan sandan ta yanke ya yi tsauri da yawa.

“Gaskiya wannan hukuncin ya yi tsauri da yawa. Allah Ya kawo musu wanda ya fi wannan,” in ji shi.

Shi ma Mustapa Sabo Alhaji na ganin laifin da suka yi bai cancanci kora ba.

“Maganar gaskiya ba a kyauta ba tun da ba kowa suka harba ba. An ce kawai sama suka harba. Hukuncin ya yi tsauri,” a cewarsa.

Wani dan Nijeriya mai suna Chibueze a shafinsa Twitter ya ce hakan bai dace ba.

“Me ya faru da dakatarwa da sake daidata tunani da kuma rage girma? A ganina, korarsu kai tsaye ya yi tsauri da yawa. Na fahimci cewa rundunar ‘yan sanda na son ta yi abin da zai zama izina ga sauran mutane ne,” a cewarsa.

“’Yan sanda na da dokokinsu, amma a ganina wannan laifin bai cancanci kora ba. Da rage girma ya fi,” a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

A shekarar 2020 an yi zanga-zangar neman soke rundunar ‘yan sanda mai yaki da fashi da makami da aka fi sani SARS bisa zargin cin zarafi matasa, lamarin da ya janyo rikici da ya haddasa rasa dukiya da rayuka.

Ita dai rundunar ‘yan sandan Nijeriya tana ba da sanarwar hukunta jami’anta da aka samu da laifin yin ba daidai ba daga lokaci zuwa lokaci.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here