UNICEF: ‘Tashin hankali bai kare ba’ bayan shekara tara da sace ‘yan matan Chibok

0
135

Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya ce tasirin da rashin tsaro ke yi a kan harkar ilimi a Nijeriya abin daga hankali ne kuma akwai yiwuwar illar hakan ta shafi al’ummomin gaba.

A wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma’a da ake cika shekara tara da mayakan kungiyar Boko Haram suka sace ‘yan matan makarantar sakandaren Chibok a Jihar Borno da ke arewa maso gabshin Nijeriya, UNICEF ta ce har yanzu akwai ‘yan matan da dama da mayakan ba su saka ba tun lokacin.

Mayakan Boko Haram sun sace dalibai ‘yan mata 276 ne a cikin wani dare a harin da ya daga hankalin duniya.

Hukumomin Nijeriya sun yi kokarin ceto da yawa daga cikin ‘yan matan yayin da ‘yan bindigar kuma suka sako wasu da kansu.

Amma UNICEF ta ce “har yanzu akwai sauran matan 96 a tsare a hannun mayakan, kuma ana ci gaba da take hakkokin dubban yara.”

Hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwarta cewa tun bayan harin makarantar Chibok, kungiyoyin masu tayar da kayar baya sun ci gaba da saka yara a cikin harkokinsu.

Ta yi kira ga dukkan masu hannu a rikicin da ke faruwa a arewa maso gabashin Nijeriya da su “girmama dokar kasa da kasa ta martaba dan adam da dokar kare hakkokin mutane da kuma kula da yara.”

“Abin da ke faruwa din yana da daga hankali. Shekara 10 kenan tun bayan sace ‘yan matan Chibok mai firgitarwa, kuma har yanzu ba a daina ganin tashin hankalin ba don ana ci gaba da sace yara da tursasa musu shiga kungiyoyin, da kashe su da ji musu rauni – ana kuma lalata rayuwarsu ta gaba,” a cewar Cristian Munduate, wakiliyar UNICEF a Nijeriya.

“Ba zai yiwu mu rufe ido kamar ba ma ganin wahalar da yara ke sha ba a Nijeriya. Dole mu yi bakin iyawarmu don tabbatar da cewa yara sun girma cikin tsaro da samun ilimi da cimma damar su,” ta kara da cewa.

Nijeriya tana shan fama da satar mutane da masu tayar da kayar baya ke yi irin su Boko Haram da Daesh a Yammacin Afirka da kuma gungu-gungun masu aikata miyagun laifuka da ke neman kudin fansa.

Ana yawan kai hari makarantu inda aka sha sace yara a kada su dazuzzuka.

Hukumar ta ce ta dukufa wajen tabbatar da cewa “kowane yaro a Nijeriya zai iya samun hakkokinsa ya zauna cikin aminci a al’ummar da za ta bunkasa.”

UNICEF “tana maraba da yarjejeniyar Gwamnatin Nijeriya ta zuba jarin naira biliyan 144.8 don Shirin Samar wa Makarantu Tsaro na 2022,” sanarwar ta kara da cewa.

Asusun Kula da Yaran ya ce “a shirye yake ya bai wa gwamnati goyon baya” a kokarinta na dabbaka tsarin “don tabbatar da cewa dukkan yaran da suka samu kansu a hannun ‘yan bindiga ko aka sako su, a mika su ga iyalansu su kuma ci gajiyar shirye-shiryen sake mayar da su cikin al’umma da gyara tunaninsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here