An daure wata mai POS saboda satar kudi

0
203

Wata kotun majistire da ke Ota jihar Ogun ta daure wata mai POS mai suna  Salawudeen Ayomide, na tsawon wata uku, saboda kama ta da laifin satar naira 120,000 mallakar wadda ta dauke ta aiki.

‘Yansanda sun binciki Ayomide, wadda  bayaninta ya nuna ba ta san wanda ya dauki kudin ba.

Da take yanke hukunci mai shari’a Misis A. O.Adeyemi ta ba wadda ake zargin zabin tara ta naira 3,000 sannan kuma za ta biya kudi naira 120,000 ga wadda ta kawo kara Nosiru Jayeola.

Tun da farko, dansanda mai gabatar da kara, Insifeto E.O. Adaraloye, ya gaya wa kotu cewa, wadda ake zargin ta aikata laifin a Ogba Ayo.

Adaraloye ya ce, laifin ya saba wa sashi na 390(9) na dokokin manyan laifuka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here