Gwamnatin tarayya ta amince da fara amfani da allurar riga-kafin zazzabin Maleriya wanda Jamiāar Oxford da ke Birtaniya ta samar.
Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta kasa NAFDAC ce ta ba da izinin amfanin da riga-kafin duk da cewa Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da sauransu ba su kammala bincike kan rashin hadarinsa ga dan Adam ba.
Da haka Najeriya ta zama kasa ta biyu a nahiyar Afirka da ta amince da riga-kafin, bayan kasar Ghana.
Rahoton WHO ya nuna a shekarar 2021 Najeriya ce kasar da ke dauke da kashi 27% na masu maleriya da kuma kashi 32% na wadanda ta yi sanadin mutuwarsu a duniya.
A ganinka samar da allurar rigakafi shine zai kawar da zazzabin a Nigeriya?
Wacce hanya kuke ganin ya kamata abi wajen kawar da Maleriya a kasar nan.