Kwararru a fannin kiwon lafiya a Najeriya sun bayyana damuwa kan yadda ake samun karuwar masu kamuwa da cutar kansar baki a kasar.
Masana harkar lafiyar sun alakanta karuwar cutar da rashin daukar kula da baki da muhimmanci da mafi yawan mutane ke yi musamman a yankunan karkara.
Hakan na zuwa ne a yayin da Ma’aikatar Lafiya ta kasar ta ce cutar kansar baki na kashe a kalla mutum 746 duk shekara a Nijeriya sakamakon rashin ziyartar cibiyoyin lafiya a kan lokaci.
A yayin da yake jawabi a taron horarwa kan hanyoyin kula da baki da Gidauniyar Cleft and facila Deformity CFDF ta gudanar a karshen makon jiya, Ministan Lafiya na Nijeriya Dakta Osagie Ehanire ya ce adadin masu kamuwa da cutar sankarar baki kan kai 1,146 a duk shekara a kasar.
Yadda ake kamuwa da ita
“Cutar sankarar baki wani nau’in ciwon daji ne da ke shafar sassan bakin dan adam kamar lebe da dasashi da hakori da harshe da makogwaro da cikin kumatu da handa da ganda da dai sauransu,” a cewar Dakta Muhammad Adam na Babban Asibitin Birnin Kudu da ke jihar Jigawa a Nijeriya.
A hirarsa da TRT Afrika, Dakta Adam ya ce cutar ta fi shafar maza da kuma wadanda shekarunsu suka haura 50, sannan ta fi yawa a kasahen fararen fata.
Likitan ya bayyana wadansu abubuwa da ka iya jawo cutar kamar “sinadarin nicotin da ke cikin taba sigari ko tabar hayaki ta shisha ko kuma tabar taunawa, da shan giya da kayan maye da kuma kwayar cutar virus mai suna HPV (human papilloma virus).
“Kazalika ana gadonta daga iyaye da kakanni, da yawan shiga matsananciyar rana a kasashen fararen fata, da rashin garkuwar jiki mai karfi, duk suna cikin hanyoyin da ake kamuwa da cutar,” in ji likitan.
Dakta Razina Abbas Kwararriyar likitar kula da baki ce a cibiyar sashin kula da baki ta Jami’ar Ahmadu Bello ABU da ke Zaria, ta gaya wa TRT Afrika cewa rashin wanke baki yadda ya kamata bayan an ci abinci ma ka iya jawo cutar.
“Saboda kwayar cutar bakteriya na iya zama a cikin bakin kuma ta haifar da matsalar cutar kansa.”
“Kuma ire- iren abincin da ake ci ba tare da wanke baki da sinadaren da ya kamata ba ya sa ake dada samun karuwar cutar a Nijeriya,” a cewar Dakta Razina.
Shi ma Dakta Adam ya jaddada cewa rashin kula baki da mafi yawan mutane ke yi musamman a yankunan karkara na ta’azzara lamarin.
”Baki na daga cikin sassan jiki masu muhimmanci kuma idan ba a kula da shi ba za a iya fuskantar matsala domin yawancin cututtuka na shiga jikin dan adam ne ta baki.
Hanyoyin magance ko takaita cutar
Kwararru sun ce idan an gane ta da wuri kafin ta yadu ana warkewa.
Amma idan ta yadu yawanci nakasa mutum take har zuwa mutuwa, a cewarsu.
Akwai hanyoyin da za ka iya bi wajen kare kanka daga kamuwa da cutar in ji Dakta Muhammad Adam.
- Daina amfani da sinadaran nicotin da ke kunshe a taba sigari da sauransu da aka ambata a baya
- Daina shan giya da kayan maye
- Yin rigakafin cutar HPV
- Yawan cin kayan lambu kamar manyan lemon tsami da karas don za su taimaka wajen gyara baki
- Wanke baki da sinadarin Floride zai taimaka wajen kashe kwayoyin cuta da ke iya cutar da baki
- Zuwa asibiti don duba sassan cikin baki musamman bangaren likitocin baki da hakori, duk bayan wata shida ko kuma ko da sau daya a shekara
- Yawan wayar da kan al’umma.
An ware kowane watan Afrilu na duk shekara a matsayin watan wayar da kan al’umma kan cutar sankarar baki.
An yi hakan ne don likitoci da kwararru a fannin kula da baki su dinga haduwa suna fadakar da mutane illar da ke tattare da cutar da hanyoyin magance ta, da kuma inda aka kwana game da yaki da ake yi da ita.