Wani muhimmin kudurin doka da Majalisar Dokokin Najeriya ta gabatar na yanke hukuncin daurin shekara 10 ga masu tallata shirye-shiryen saka hannayen jari “na damfara” da aka fi sani da Ponzi Scheme, ya samu karbuwa sosai a kasar.
Ana kallon dokar a matsayin wadda ke da matukar muhimmaci kuma wadda ake bukata wajen bai wa mutane kariya daga ‘yan damfarar da ke yaudararsu don zuba hannun jari a cikin wani shiri ko kasuwanci a bisa alkawarin samun riba gwagggwaba.
Matakin na zuwa ne bayan da masu tallata shirye-shiryen saka hannayen jari na PONZI suka damfari miliyoyin ‘yan Najeriya wadanda suka tafka hasarar dukiya mai tarin yawa.
Kididdiga ta nuna cewar ya zuwa shekarar 2022 cikin shekara biyar da suka gabata, ‘yan Nijeriya sun tafka asarar sama da Naira biliyan 300 a ayyukan damfara na Ponzi, kamar yadda wani rahoto na cibiyar da ke sa ido a kan zuba hannun jarin kudade ta Norrenberger Financial Investments ya nuna.
Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya Ahmad Lawan, ya ce kudirin dokar zai kare masu zuba jari ta hanyar daidaita kasuwa da kuma rage hadurran da ke cikin kasuwanci, baya ga zartar da hukuncin da ya dace akan masu tallata shirin na Ponzi.
Hassan Sardauna Yamayo, wani mai sharhi kan al’amuran yau da kullum kuma kwararre kan hada-hadar kudi, ya ce kudirin dokar mataki ne mai matukar muhimmanci a tarihin Nijeriya.
“Ayyukan damfara sun zama ruwan dare a sassa daban-daban a Nijeriya, walau ‘yan Yahoo-Yahoo ne ko masu satar bayanai ko ‘yan zamba cikin aminci ko kuma masu tallata shirin saka hannayen jari na Ponzi. Duka suna bukatar a yi maganinsu.”
Da yake bayyana ra’ayinsa yayin zantawa da TRT Afirka, Yunusa Abubakar, wani dan Majalisar Wakilai ya ce ana sa ran kudirin zai taimaka wajen gudanar da harkokin kasuwanci ba tare da matsala ba a Nijeriya, lamarin da zai taka rawa wajen karfafa tattalin arzikin kasar.
Yayin da kudurin dokar ya samu karbuwa a zauren Majalisar Dokokin Nijeriya, har yanzu akwai sauran aiki, domin kuwa yana bukatar amincewar shugaban kasa kafin ya zama doka.
Hukumar kula da harkokin hada-hadar kudade da hannayen jari ta Nijeriya, ta ce ‘yan kasar miliyan uku ne suka tafka asarar naira biliyan 18 a dunkule, a lokacin da aka yaudare su da shiga shirin kasuwancin juya kudade na MMM, wato Mavrodi Mundial Movement, a shekarar 2016.
Sai dai duk da waccar asarar, hakan bai hana masu tallata shirye-shiryen saka hannayen jari na damfara cigaba da samun karbuwa ba, abin da ya sa suka ci gaba da cin karensu babu babbaka wajen damfarar dumbin mutane da ke zuba kudadensu cikin shirye-shirye ko kasuwancin da aka lallube kura da fatar akuya.
Annoba ta Damfara
Kusan dukkanin shirye-shiryen ‘yan damfara na Ponzi suna amfani da dabarun kirkirar wani tsari da ke nuna samun riba mai yawan gaske, ko kuma kashi 100 bisa 100 wajen jan hankalin mutanen da suke yi wa allkawarin za su samu amfani mai yawa bayan wani dan lokaci.
Wani masani kan harkokin tsaron intanet Yusufdeen A Yusuf ya ce yaduwar dabarun ‘yan damfarar “abin ban tsoro ne kuma abin damuwa a Nijeriya,’’musamman la’akari da yadda mutane da dama ke hankoron ganin sun samu kudi ta hanya mai sauki.
Zainab Shehu daya ce daga cikin miliyoyin ‘yan Nijeriya da ta saka kudadenta a irin shirin, wanda ya kai ga yaudara.
Ta yi asarar akalla Naira 700,000 bayan wata kawarta ta gabatar mata da wani kasuwanci ta intanet.
“A karon farko naira 100,000 na biya, bayan mako biyu suka rubanya min abin da na bayar. Na yi farin ciki sosai, don haka bayan samun wasu kudaden sai na yanke shawarar zuba naira 500,000, daga lokacin ne na fada tarkon ‘yan damfarar don kuwa har zuwa yanzu babu uwar kudin ballantana riba,’’ ta fada cikin takaici.
A halin da ake ciki dai ta sha alwashin cewa ba za ta sake saka jari a cikin wani kasuwancin ba, tare da bayyana fatan ganin sabuwar dokar da ake shirin kafawa ta dakile yawan damfarar mutanen da ake yi.
Ita ma Fauziyya wacce ta tafka asarar sama da Naira 500,000 a cikin shirin ‘yan damfarar na Ponzi har guda biyu, ta ce mafi munin lamarin shi ne damuwa mai zurfi da ta shiga.
‘’Ba zan taba bai wa wani shawara ya zuba kudinsa cikin jarin masu yi wa mutane romon baka da zummar saka jari ba, domin neman kudi mai sauki ba ya haifar da sakamako mai kyau,’’ ta yi gargadi.
Mataki na gaba
Mataki na gaba shi ne a sake tantance yadda dokar da ake son aiwatarwa don tsefe dukkanin abin da ta kunsa ta yadda idan akwai bukatar yi mata kwaskwarima sai a yi wato “Bill cleaning,’’ kamar yadda dan majalisa Abubakar ya bayyana.
Za a yi haka ne kafin a aika wa shugaban kasa, wanda ke da wa’adin kwana 30 ya rattaba hannu kan kudirin don mayar da shi doka a kasar.
Idan har shugaban kasa ya ki sanya hannu a kan kudirin, dole ne ya bai wa majalisar dokoki kwararan dalilai na kin yin hakan.
‘’Idan majalisa ta amince da hujjojin shugaban kasa, to sai a gyara dokar, idan kuma har ba a yi wa dokar gyara ba, kuma shugaban kasa bai ba da amsa ba bayan kwana 30, Majalisar Dokoki na da ‘yancin tabbatar da dokar” a cewar dan Majalisar Wakilai Abukakar Yunusa.
Wannan furucin na dan majalisar ya kawo fata ga wadanda abin ya shafa kamar su Fauziyya da Zainab, wadanda suka dade suna jiran ganin an daure ‘yan damfarar a gidan yari.
Sai dai babban abin tambaya a nan shi ne Didan wannan kudiri ya zama doka, shin zai kawo karshen laifukan zamba ko kuma tasirinta zai tsaya ne wajen wayar da kan al’umma kawai?
“Ayyukan damfara irin wannan suna da mummunan tasiri ga mutane da kuma tattalin arziki. Ina da kwarin gwiwar cewa kudirin zai kawo sauyi, ko da kadan ne, musamman ma a daidai lokacin da damfarar ke kara habaka fiye da kowane lokaci,” a cewar wani mai fashin baki Yamayo.
Da yake yabawa majalisar kan matakin farko da ta dauka, ya bukaci wakilan da su tabbatar da cewa dokar hukunta masu zamba ta shafi kowa, ba tare da la’akari da matsayi ko siyasa ba.
Shi ma masanin harkokin tsaro na intanet Yusuf, ya gamsu da cewa kudirin dokar zai dakile kamfanonin kasuwanci iri na Ponzi a Nijeriya.
Ya kuma kara da ba da shawarar cewa kamata ya yi hukumomi su mayar da hankali wajen kara wayar da kan ‘yan Nijeriya game da illolin da ke tattare da neman kudi cikin gaggawa.
“Idan har aka yi nasarar wayar da kan ‘yan Nijeriya suka gujewa yaudarar ‘yan damfara da ke nuna musu hanyoyin yin kudi cikin sauki, hakan zai taimaka matuka wajen dakile matsalar,” ya shaida wa TRT Afrika.