Wasu yankunan Afirka na fuskantar barazanar yunwa – MDD

0
108

Yayin da sama da mutane miliyan 41 ke fuskantar tsananin talauci a lokacin rani, musamman a bana, Majalisar Dinkin Duniya ta ce, matsalar karancin abinci na kara ta’azzara a yammaci da yankin tsakiyar Afirka.

Rahoton bankin duniya ya yi kiyasin, cewa mutane miliyan 29 a halin yanzu sun dogara da taimakon abinci na gaggawa.

Cibiyar hada-hadar kudin ta duniya, ta dora alhakin yawaitar matsalar karancin abinci mai gina jiki a yankin kan tabarbarewar tashe-tashen hankula, da yawan talauci, da saurin sauyin yanayi, karancin amfanin noma, da gurbacewar muhalli.

Gargadin na baya-bayan nan game da karancin abinci ya kuma kara da cewa hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa mutane miliyan 48 a kasashen yammaci da tsakiyar Afirka rayuwar su ke cikin hatsari, a kokarin dakile hauhawar farashin kayayyaki da ke haifar da karancin abinci.

Don magance wannan, bankin duniya ya ce ya dauki wani tsari na samar da abinci, musamman mai gina jiki, ta hanyar samar da kudade daga ayyukan da ake ci gaba da gudanarwa, da kafa  bangaren bayar da agajin gaggawa, tattara kudaden ba da agajin gaggawa daga cibiyar Bayar da Tallafin ta Musamman, da kuma yin aiki tare da masu aikin jin kai don sa ido kan matsalar rashin abinci.

Ana sa ran shirin zai lakume dala miliyan 766 a Yammacin Afirka kadai, inda sama da mutane miliyan hudu a fadin yankin za su amfana da shi.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, shirin zai yi dukkan mai yuwu wa wajen inganta aikin noma ta hanyar amfani da fasahohin zamani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here