Kuɗin-cizo sun cinye mutum da ransa

0
97

Ana zargin cewa ‘ƙwari da kuɗin-cizo sun cinye wani mutum da ransa.

Mutumin dai fursuna ne a wani gidan yari da ke Atlanta na ƙasar Amurka.

An ɗaure Lawshawn Thompson bayan kama shi da laifi, inda aka ajiye shi a ɓangaren kula da masu lalurar ƙwaƙwalwa na gidan yarin yankin Fulton, bayan da aka gane cewa yana da taɓin hankali.

Lauyan iyalin marigayin, Michael D Harper ya bayyana wasu hotuna da suka nuna yadda kuɗin-cizo ya baibaye gawar mamacin.

Lauyan na neman a gudanar da bincike, kuma ya ce akwai ƙara da ya shigar.

A wata sanarwa, Mr Harper ya ce “An gano gawar Mr Thompson a cikin wani ɗakin gidan yari da ya yi kaca-kaca, bayan da ƙwari da kuɗin-cizo suka cinye shi.”

Ya ƙara da cewa “Dakin da aka ajiye Mr Thompson bai cancanci a ajiye koda dabba ce maras lafiya ba. Bai cancanci haka ba.”

Rahoton likita mai bincike na yankin Fulton ya ce, an gano Mr Thompson ne ba ya motsi a ɗakinsa na gidan yari a ranar 19 ga watan Satumba – wata uku bayan kama shi – inda daga ƙarshe aka tabbatar cewa ya mutu, bayan da jami’an lafiya suka kasa farfaɗo da shi.

CBS News ta ruwaito Mr Harper na cewa, bayanan kula da lafiya na Mr Thompson sun nuna cewa jami’an gidan yari da masu kula da lafiya sun lura cewa lafiyar marigayin na tabarbarewa, amma ba su ɗauki matakin taimaka masa ba.

Rahoton jami’in kula da lafiyar ya nuna cewa ‘akwai dandazon kuɗin-cizo a ɗakin masu lalurar kwakwalwa da marigayin ke ciki, sai dai babu wata alama ta ƙarara da ta nuna cewa Mr Thompson ya shiga cikin wani mummunan hali.

Rahoton ya ce har yanzu ba a tantance sanadin mutuwar tasa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here