Manchester City ta samu damar haduwa da Real Madrid a matakin dab da na karshe na gasar Zakarun Turai na kakar bana bayan ta cire Bayern Munich a gasar a wasan da suka yi jiya da daddare a Jamus.
Fatan kocin Bayern Munich, Thomas Tuchel, na doke City bai cika ba don ‘yan wasan Bayern sun kasa farke kwallaye uku da City ta zura musu a raga a karawarsu a Etihad.
Maimakon haka, madugun City, Erling Haaland ne ya tabbatar da ficewar Bayern daga gasar zakarun Turai a lokacin da ya zura kwallo a ragar Bayern minti 57 da fara wasa.
Duk da cewar Joshua Kimmich ya farke wa Bayern Munich kwallo daya ta hanyar fenareti a miniti na 83, bai hana ficewar kulob din na Jamus daga gasar Zakarun Turai ba.
Wannan sakamakon na nufin City za ta kara da Real Madrid, wadda ta cire ta daga gasar a bara.
Yadda Madrid ta doke City a bara
A kakar bara a wasa na biyu na matakin dab da na karshe ne Real Madrid ta cire Man City daga gasar Zakarun Turai.
An fara wasan da aka yi a Bernabeu ne yayin da City ke kan gaba daga sakamakon wasan da suka yi a Etihad, sai kuma Madrid ta juya akalar wasan inda ta doke City da 3-1.
Lamarin ya mayar da jimillar kwallayen da aka ci a wasanni biyu na matakin dab da na karshe 6-5.
Da wannan sakamakon ne Real Madrid ta fitar da Man City.
Kungiyar ta Madrid ta je wasan karshe na gasar inda ta doke Liverpool kuma ta dauki kofin Zakarun Turai a karkashin jagorancin Carlo Ancelotti.
Daukar fansa
Kocin City, Pep Guardiola, wanda ya taba aiki a matsayin kocin Barcelona, babbar abokiyar hamayyar Madrid a gasar La Liga ta Sifaniya, ya ce ya san City za ta hadu da Madrid.
“Duk kulob sun san idan kana son ka dauki kofin Zakarun Turai dole sai ka doke Madrid,” a cewar Guardiola.
“Ina fatan hakan zai faru,” in ji Bernardo Silva a lokacin da aka tambaye shi kan yiwuwar daukar fansa a kan abin da Madrid ta yi wa City a kakar da ta gabata.
“Lallai za mu fito neman nasara. Kullum abin da muke nema kenan, amma a halin yanzu ina ganin ‘yan wasanmu suna da kwarin gwiwa sosai. Ina ganin za mu yi nasara.
Silva na ganin da irin ‘yan wasa masu zura kwallo a raga kamar Haaland kulob dinsa zai yi nasara a zagayen dab da na karshe.
Sai dai ita ma Real Madrid ba kanwar lasa ba ce.
Ita ce ta fitar da Chelsea daga gasar Zakarun Turai a kakar bana bayan ta doke Blues da ci hudu da nema a wasannin biyun da suka yi a matakin kwata fainal
A halin yanzu ita ce ta biyu a teburin gasar La liga, kuma yaran Carlo Ancelloti za su nemi su nuna wa yaran Pep Guardiola cewar nasarar da suka yi a kansu bara aba ce wadda za su iya maimaitawa.
Sai kungiyoyin biyu sun hadu a ranar 9 da ranar 17 ga watan Mayu ne za a san kugiyar da za ta kai ga wasan karshe na gasar zakarun Turai ta kakar bana.