Ma’aikatar Lafiya ta kasar Japan ta amince da amfanin da kwayoyin zubar da ciki na farko da aka samar a ƙasar.
A halin yanzu dai, matan da ke neman zubar da ciki ba za su iya yin hakan ba sai ta hanyar tiyata.
Ƙwayoyin waɗanda wani kamfanin Burtaniya ya sarrafa, za a iya amfani da su wajen zub da cikin da ya kai har makonni tara.
Sai dai har yanzu maganin na jiran amincewa ta karshe, bayan an gama tattaunawa kan farashi da kuma ka’idojin amfani da shi.
Ana yi wa wannan matakin kallon wani ci gaba ta fuskar ba mata damar yin zabi wajen haihuwa a Japan.