Adadin kudaden da Najeriya ta ciyo bashin su daga bankin duniya ya kai naira triliyan 6, abin da ke nufin adadin ya karu da kaso 121.46, karkashin gwamnatin shugaba Buhari.
Bayanai sun ce kasashen da biyar da bankin ya fi bin bashi sun dan rage yawan kudaden da ake binsu amma banda Najeriya.
Tuni dai masana tattalin arziki suka fara hasashen cewa gwamnati mai zuwa a kasar na iya fuskantar kalubalen biyan basussukan da ake bin Najeriya idan ba a dauki matakin da ya dace wurin rage yawan cin bashin da ake yi yayin da kasar ke fama da karancin kudin shiga.