‘Yan sanda sun cafke mutum biyu bisa zargin garkuwa da mutane a Adamawa

0
175

Jami’an ‘yan sanda tare da hadin guiwar wasu mafarauta a Mubi ta Arewa, sun yi nasarar cafke wasu mutane biyu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne.

‘Yansandan da ke aiki a hedikwatar ‘yan sanda ta Mubi ta Arewa sun samu wani rahoto game da yin garkuwa da Aisha Ahmadu ‘yar shekara 28, wacce aka harbe mijinta, Alhaji Ahmadu Mohammed a yayin da masu garkuwar ke aikata ta’asarsu a ranar 3 ga Afrilu, 2023 a kauyen Digil da ke karamar hukumar Mubi ta Arewa.

Bincike kan rahoton ya kai ga cafke Mohammed Bello mai shekaru 22 da Abubakar Mallam mai shekaru 26 da haihuwa wadanda dukkansu mazauna karamar hukumar Mubi ta Arewa ne.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Suleiman Yahaya Nguroje a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya ce dukkan wadanda ake zargin sun hada baki ne, suka shirya sace matar sannan kuma suka kashe mijinta.

Sun tsare matar har na tsawon kwanaki uku har sai da aka biya kudin fansa Naira Miliyan biyu da rabi (N2,500,000).

Kwamishinan ‘yansandan, CP Afolabi Babatola, ya yabawa DPO na hedikwatar ‘yansandan da ke Mubi ta Arewa da jami’ansa bisa yadda suka dakile hanyar bata gari masu aikata miyagun laifuka, ya kuma bukace su da su ci gaba da gudanar da ayyukansu na Basira.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here