Idan Messi ya bar PSG ina ya kamata ya koma?

0
131

Alamu suna ci gaba da nuna cewa shahararren dan wasan nan dan asalin Argentina, wato Lionel Messi zai bar kulob dinsa na yanzu, wato Paris Saint Germaine, PSG na Faransa.

Akwai kungiyoyi masu farautar Messi wanda ake kyautata zaton zai sauya sheka a kakar siyan ‘yan wasa a lokacin bazara mai zuwa.

An jiyo a karo na hudu, masoya Barcelona a filin wasa na sun daina wakar yabon kungiyara a daidai minti na 10 da wasansu na baya-bayan nan da Atletico Madrid ranar Lahadi.

Kamar yadda shafin wasa na Goal.com ya ruwaito, a maimakon wakar kulob din, masoyan sun yi ta wakar yabon Lionel Messi, suna nuna fatansu nay a komo taka leda a Barcelona.

Jami’an kungiyar su kansu sun bayyana burinsu na dawo da Messi zuwa Camp Nou, inda a ‘yan kwanakin nan suka ce tattaunawa tana ci gaba da gudana da wakilan dan wasan.

Ana sa ran albashin Messi zai kai kamar kwatankwacin wanda yake karba a yanzu a PSG, wanda ya kai dala miliyan 41 a shekara.

Sai dai kuma, Messi zai fi son zuwa kulob din da zai buga wasan zakarun Turai, kuma yake da damar cin kofin gasar kasa. Wannan ne zai hana da yawan kulo din da ke Turai, yayin da ‘yan tsararu ne ke iya cika wannan ka’aida.

Amma ba idan ban da Barcelona, in Messi zai buga wasa? Goal.com ya kalli wasu daga cikin zabin da Messi yake da shi.

Manchester City

Bayan Barcelona, Manchester City ce za ta zo ta biyu a zabin da Messi ya kamata ya duba. Za a iya cewa kocin Man City na yanzu, Pep Guardiola shi ne ya fito da hazakar Messi lokacin suna Barcelona.

Sai dai akwai kalubalen dangane da inda ya dace Guardiola ya saka Messi, kasancewar a yanzu hankalinsa yank an dan wasan gaba dan asalin Norway, Erling haaland.

Haka kuma, duk da ana sa ran tafiyar Ilkay Gundogan da Bernardo Silva a wannan bazarar, Messi ba shi ne mafi dacewa ba don canjin dayan ‘yan wasan biyu.

Amma dai tabbas, Guardiola shi ya san inda ya fi dacewa ya saka Messi a jerin ‘yan wasan nasa.

Manchester United

Machester United tana kokawa kan rashin ‘yan wasan gaba masu iya cin kwallo sanda ake bukata. Amma uma koci Erik ten Hag yana ji da Bruno Fernandes da kuma Marcus Rashford wanda ya dawo kwanan nan.

Yayin da aka sa ran Man United za ta fitar d kudin siyan ‘yan wasa, akwai batun masu kulob din, wato Glazers, wadanda ba su nuna hanzari wajen cefanar da kulob din ba zuwa yanzu.

Sai dai akwai yiwuwar su mayar da hankali kan siyo dan wasan Napoli, Victor Osimhen ko Harry Kane na Tottenham.

Chelsea

Lokaci na karshe da Chelsea ta yi yunkurin siyan babban dan wasa, abin ya kai ga korar kocinta. Amma messi wanda yake da shekaru 36, ya bambanta da yanayin Cristiano Ronaldo.

Amma dai Chelsea za ta yi kora ‘yan wasa da yawa, saboda da alama irinsu Mason Mount, da Conor Gallagher, da Christian Pulisic, da Hakim Ziyech, da N’Golo Kante da Pierre-Emerick Aubameyang.

Kari kan haka, Joao Felix zai iya mayar da zamansa na aro zuwa dindindin, wanda zai sa Chelsea ta bukaci sabon dan wasa mai basira.

Yayin da ake tunanin Chelsea za ta dauko tsohon kocin Messi a PSG, Mauricio Pochettino, wanda shi ma dan Argentina ne, ya bayyana cewa yana jin dadin wasa da Messi.

Bayern Munich

A yanzu Bayern tana fama da matsala karkashin koci Thomas Tuchel mai alaka da cin wasa, inda a yanzu aka fitar da shi daga gasar zakarun Turai, kuma suka fado zuwa mataki na biyu a gasar Bundesliga.

Dalilan da Bayern ke samun rashin nasara suna da yawa, amma karancin da rashin ingancin ‘yan wasan gaba yana cikinsu.

Duk da dai irin wannan matsala, mutum day aba ya iya warware ta, sako Messi zai iya tallafawa yunkurin sabon kocin na sake gina kungiyar.

Amma Bayern tana da matsalar kashe kudi, saboda ta gaza fitar kudi don siyan Haaland dan shekara 21 a baya. Wannan ya sa da kamar wuya, su fito da kudi yanzu don siyan dan wasan da ya kama hanyar 40.

Newcastle

Duk da ba a tunanin komawa Messi zuwa karamin kulob kamar Newcastle, kasanacewar kulob kadan ne ke da karfin arzikin siyansa, wanda Newcastle tana ciki.

Wannan ba batu ne na tayin kudi ba kawai saboda Newcastle ta samu zuba jari daga hamshakan masu kudi daga Saudi Arabia. Hakan ya sa ana sa ran kulob din zai taso ya zama babba a gasar Firimiya nan da shekaru masu zuwa.

Alamu sun nuna Newcastle za su buga wasan zakarun Turai a badi, don haka ake ganin za su siyo dan wasa mai shuhura a duniya nan ba da dadewa ba.

Inter Miami

Akwai yiwuwar Messi ya yi watsi da yin wasa a Turai gabakidaya. Wannan ya janyo ana hasashen ya koma Amurka, duk kuwa da rade-radin zai koma Barcelona.

Haka nan alamu sun nuna hakan zai iya faruwa bisa la’akari da shirin yadda jagororin gasar zuka sha alwashin hada kudin da za su iya kawo Messi zuwa Amurka.

An fi ganin wannan hasashe zai tabbata a karshe, amma dai sai nan da shekara daya ko biyu, saboda Messi yana da sauran gudumowar bayarwa a Turai. Kuma ana sa ran zai ci gaba da buga gasar Copa America a 2024.

Al-Hilal

Kulob din Saudiyya na Al-Hilal sun bayyana a fili cewa suna burin su fitar da kudin siyan Messi.. A ruwaito cewa sun yi tayin bai wa Messi kwantiragi da zai ninka wanda aka ba Ronaldo a Al-Nassr, wato wajen dala miliyan $215.

Hakika, akwai tunanin kasuwanci kan wannan tayin. Ronaldo zai kasance a Saudiyya har akalla 2024, matukar ba ya sauya sheka zuwa Turai ba.

Kenan idan da Messi zai amince da wannan tayi mai lagwada, shi da Ronaldo za su kara da juna wanda haka zai dauki hankali matuka.

Amma kamar gasar Amurka ta MLS, komawar Messi gasa mara farin jin kamar ta Saudiyya, abu ne mai wuya kasancewar har yanzu da sauran karfi tattare da wannan hazikin dan wasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here