An kama masu garkuwa da mutane 17 a Nassarawa

0
120

Rundunar ’yan sandan Jihar Nasarawa ta yi nasarar kama mutane goma sha bakwai da ake zargi da ayyukan garkuwa da mutane don karbar kudin fansa.

An samu nasarar kama wadanda zargin da garkuwa da mutane ne a ayyukan sintiri da samame da ‘yan sanda suka yi tun daga watan Fabrairu zuwa watan Afrilun wannan shekara ta 2023.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Nasarawa, DSP Ramhan Nansel wanda ya tabbatar da lamarin, ya ce a yayin gudanar da aikin nasu, sun kuma yi nasarar kubutar da mutane biyar da aka yi garkuwa da su, tare da kwace bindigogi hudu da albarusai takwas daga wasu wadanda ake zargin.

Ya kara da cewa binciken da suka gudanar ya nuna cewa wadanda aka kama, suna tare babbar hanyar Nasarawa Eggon zuwa Akwanga da ma cikin garin Lafia da kewaye zuwa Kudancin jihar, inda kuma suke sace mutane.

A makon da ya gabata ne tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Nasarawa, Farfesa Onje Gye Wado ya kubuta daga hannun wadansu da suka yi garkuwa dashi.

A wata tattaunawa da shi, tsohon Mataimakin Gwamnan ya bayyana cewa wadanda suka yi garkuwa da shi matasa ne da ke sana’ar kiwon dabbobi.

A cewarsa, ba ya zaton talauci ne ko rashin aikin yi ne ya sanya su shiga sha’anin garkuwa da mutane.

Dokta Mukhtar Wakeel mai sharhi kan lamuran yau da kullum ya shaida wa Muryar Amurka cewa son zuciya ne ke sanya mutane aikata miyagun laifuka.

Rudunar‘ yan sandan ta Jihar Nasarawa ta kuma sha alwashin hada kai da sauran jami’an tsaro don kakkabe bata gari a Jahar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here