Tsohon ministan kwadago Musa Gwadabe ya rasu

0
100

Allah Ya yi wa tsohon Ministan Kwadago kuma tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Musa Gwadabe rasuwa.

Ahaji Musa Gwadabe ya rasu ne a safiyar ranar Laraba bayan fama da jinya yana da shekaru 87 a duniya.

Za a gudanar da jana’izarsa a layin Madaka da ke kan tittin Maiduguri da Kano da misalin karfe 2 na rana.

Marigayin ya rasu ya bar mata biyu da ’ya’ya 11 da kuma jikoki.

Daga cikin ’ya’yansa akwai Alhaji Nazifi Musa Gwadabe, wanda dan kwangila ne a Jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here