Direbobin da suka dauko daliban Naijeriya daga Sudan sun bijirewa fasinjoji a tsakiyar Sahara

0
100

Ɗaliban Najeriya da tun farko, suka tashi daga Sudan a motocin bas-bas zuwa ƙasar Masar, sun gamu da cikas a kan hanya.

Direbobin motoci guda bakwai da suka ɗauko ɗaliban daga birnin Khartoum ne, suka buƙaci cikon kuɗaɗensu, kafin su ci gaba da tafiya.

Ɗaliban sun ce akwai mata masu shayarwa cikinsu lokacin da motocin suka tsaya a wani wuri cikin Sahara da ke yankin Dongola.

Dongola, shi ne babban birnin jihar Arewacin Sudan wato Northern Sudan a gaɓar Kogin Nilu, tana kuma da nisan kilomita 411 daga Khartoum.

Da yammacin Laraba ne sahun farko na ɗaliban Najeriya ya fara tashi a kan hanyar zuwa Aswan, tsallaken iyakar ƙasar Masar daga Sudan.

An ji muryar wani ɗalibi, ga alama daga birnin Khartoum yana tabbatar da cewa sun samu saƙonni daga takwarorinsu da suka tashi da yammacin Laraba a motoci cewa tafiyarsu ta tsaya.

Muryar ta ci gaba da cewa bayanan da suka samu, su ne kamfanonin motocin ne suka buƙaci direbobin su dakata, har sai sun karɓi cikon kuɗaɗensu daga hannun mahukuntan Najeriya.

Ana kyautata zaton cewa akwai ‘yan Najeriya fiye da 5,000 a Sudan da ke son a kwashe su zuwa gida, a ciki har da ɗalibai kimanin 3,500.

Za su yi tsawon sa’a 13 suna tafiya daga Khartoum kafin su sauka a Wadi Halfa mai ratar kilomita 30 daga kan iyakar Masar, daga nan kuma su ƙarasa Aswan a cikin Misira.

Dubban jama’a ne ke ci gaba da ficewa daga Sudan daidai lokacin da wata yarjejeniyar tsagaita ta tsawon sa’a 72 tangal-tangal, inda rahotanni ke cewa an ci gaba da jin rugugin bindigogi nan da can.

Hukumomin Masar sun ce aƙalla mutane fiye da dubu 10 ne suka tsallaka cikin ƙasar a tsawon kwana biyar tun bayan kaurewar faɗa tsakanin rundunar sojojin Sudan da mayaƙan rundunar masu kayan sarki ta RSF.

Wasu ‘yan asalin Najeriya da suka shafe shaekaru da dama suna zaune a Sudan sun bi sahun ɗaliban ƙasar da suka je karatun jami’a a ƙoƙarinsu na kuɓuta daga faɗan da ake ci gaba da gwabzawa.

Wasu rahotanni na cewa nisan tafiyar ‘yan Najeriyar zai iya ƙaruwa don kuwa da yiwuwar za su riƙa haɗuwa da sojoji da kuma jami’an tsaro masu bincike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here