An caka wa malamin addini wuka bayan kade shi da mota

0
271

Wani mutum ya caka wa wani malamin addinin Musulunci wuka a birnin Qom na kasar Iran.

Da farko sai da mutumin ya yi amfani da motarsa wajen kade wasu mutum biyu da ke tafiya, ciki har da malamin, sannan ya fito da wuka ya caka wa malamin.

Mutumin ya yi aika-aikan ne kwanaki kadan bayan an harbe wani malamin addini, Abbas Ali Soleimani — mamba ne a kwamitin zaben shugaban addini na kasar — har lahira a wani banki a lardin Mazandaran.

Jami’in dan sanda na birnin Qom, Amir Mokhtari, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na kasar (IRNA) cewa an garzaya da malamin addinin zuwa asibiti, inda aka kwantar da shi a sashen bayar da kula na gaggawa.

Amir Mokhtari ya da daya mutumin da aka kade yana asibiti tare da maharin, wanda shi ma ya ji wa kansa rauni da wukar.

Jami’in ya bayyana cewa ana gudanar da bincike domin gano manufar harin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here