Italiya: Napoli ta fara jin kamshin kofin gasar Serie A

0
119

Kungiyar Napoli ta gasar Serie A a Italiya, ta dauki hanyar lashe kofin gasar a karon farko cikin shekaru 30.

Rabon da kungiyar ta lashe kofin tun lokacin da Maradona yake buga mata kwallo.

Napoli ta lashe kofin a 1987 da 1990 a filin wasa na Stadio San Paolo, wanda yanzu aka maye gurbin sunansa da Maradona bayan da ya rasu shekaru biyu da rabi da suka gabata.

Napoli ta sanar da dage wasanta da Salernitana daga Asabar zuwa Lahadi.

Idan har Lazio ba ta ci wasanta da Inter Milan a ranar Lahadi ba, Napoli za ta samu nasara.

Kungiyar ta Napoli ta shiga wannan karshen mako da tazarar maki 17 da ta ba Lazio.

Kazalika an dage wasan Napoli da Udinese daga Talata zuwa Alhamis.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here