Dan bayan Manchester City da Ingila Kyle Walker, yana son ya ci gaba da zama a kungiyar duk da rashin sanya shi a wasa sosai a wannan kakar da kuma sha’awar É—aukarsa da Aston Villa da AC Milan ke yi. (Star)
Newcastle da Manchester City sun fice daga jerin masu neman dan wasan tsakiya na Chelsea Mason Mount, kuma ana sa ran dan Ingilan zai bar Stamford Bridge a bazara. (Football Insider)
Amma ita kuwa Arsenal har yanzu tana son Mount wanda hakan ke nufin za ta hakura da zawarcin Declan Rice na West Ham da Ingila. (Mail)
Bayern Munich kuwa na sha’awar dan gaban Aston Villa Ollie Watkins, dan Ingila a madadin Harry Kane, idan ba su samu kyaftin din na Ingila ba. (Mirror)
A shirye Arsenal take ta saurari tayi daga kungiyoyin da ke son sayen Granit Xhaka da Kieran Tierney da kuma Folarin Balogun domin samun kudin gogayyar sayen ‘yan wasan da za ta tunkari gasar Zakarun Turai da za ta koma. (Mirror)
-
2023
Aston Villa ce kan gaba a kungiyoyin da ke son sayen kyaftin din Feyenoord Orkun Kokcu a bazara, wanda wasu kungiyoyin na Premier biyar su ma suna son dan wasan na tsakiya dan Turkiyya mai shekara 22. (Mirror)
Inter Milan na shirin zawarcin dan bayan Fulham Tosin Adarabioyo, wanda shekara daya da ‘yan watanni suka rage masa a kwantiraginsa a Craven Cottage. (Sky Sports)
Tottenham da AC Milan na gogayyar sayen dan gaban Newcastle Allan Saint-Maximin amma kuma Magpies din sun sa masa farashin fam miliyan 50. (Mirror)
Harry Maguire, na ganin cewa zai bar Manchester United a bazaran nan, amma kuma yana fargabar rasa gurbinsa a tawagar Ingila kafin gasar kofin Turai ta Euro 2024. (Mail)
Arsenal na sha’awar dan bayan Crystal Palace Marc Guehi, mai shekara 22, a kokarin da suke yi na samun wanda zai taimaka wa William Saliba. (Express)
Juventus na tunanin daukar kociyan Marseille Igor Tudor idan Max Allegri ya bar su a bazara da kuma ganin cewa Antonio Conte da Zinedine Zidane da kungiyar ke so ka iya mata tsada sosai. (Mail)
Dan bayan Ajax Jurrien Timber, mai shekara 21, ya tabbatar cewa zai bar kungiyar a bazaran nan yayin da Manchester United da Liverpool ke nuna sha’awarsu a kansa. (Metro)
A shirye dan gaban Crystal Palace da Ivory Coast Wilfried Zaha yake ya tafi Marseille ta Faransa, kamar yadda aka ce dan wasan na son ganin ya taka leda a gasar Zakarun Turai. (90 min)
Mai tsaron ragar Nottingham Forest wanda Manchester United ta ba su aronsa Dean Henderson, yana son barin United din gaba daya a bazara saboda golan na Ingila na son ya rika wasa akai-akai. (Football Insider)
Manchester City da Brentford na tattaunawa da AFC Wimbledon domin sayen matashin mai tsaron ragar tawagar Ingila ta ‘yan kasa da shekara 16 Thorsten Brits. (Fabrizio Romano)
Liverpool ta fara tattaunawa da Sporting Lisbon domin sayen dan wasanta na tsakiya Manuel Ugarte, dan Uruguay mai shekara 22, wanda Sporting din ta yi wa farashi fam miliyan 53, kuma Leeds da Tottenham da Aston Villa ma na sonshi. (O Jogo)
Manchester United da Newcastle United da kuma Liverpool dukkaninsu na son dan bayan Nice, ta Faransa, Jean-Clair Todibo wanda aka yi wa farashi fam miliyan 26.5, a bazaran nan. (L’Equipe ).