Wani matashi da ya yi wata yarinya ’yar shekara biyar fyade a cikin masallaci ya shiga hannun hukuma.
Jama’ar gari sun cafke matashin, wanda ake zargin dillalin muggan kwayoyi ne, bayan ya lalata yarinyar ta gaba da baya a cikin masallacin da tsakar rana, a unguwar Kabul da ke garin Kayeri na Karamar Hukumar Fune ta Jihar Yobe.
Dubun matashin mai shekaru 18 ta cika ne bayan da ya aiki yarinyar ta sayo masa goro, amma daga baya ya faki idon jama’a, ya bi ta ya yi mata fyade a cikin kangon masallacin.
Majiyarmu da ke wurin da aka matashin ta ce, “Yayin da yake aikata wannan aika-aikar tasa, sai ya ji karar mai wucewa kuma ya yi kokarin guduwa amma aka kama shi kuma aka tilasta masa ya ba da labarin abin da ya aikata.”
Yayinyar ta ce sai da ya shigar da ita cikin kangon masallacin ya tube ta haihuwar uwarta, sannan ya zakke mata, da karfin tsiya.
Ta bayyana cewa ta raka yayarta mai kimanin shekaru tara tallan goro ne lokacin da matashin ya kira ta ya aike ta, amma daga bisani ya bige da yi mata wannan aika-aika.
A cewar majiyarmu, yarinyar ta yi ta zubar da jini babu kakkautawa, sakamakon rauni da ta samu a matuncinta da kuma duburarta.
Tuni dai aka mika wanda ake zargin ga ’yan sanda a garin Damagum, hedikwatar Karamar Hukumar Fune, domin gudanar da bincike da kuma gurfanar da shi a gaban kuliya don girban abin da ya shuka.