An yi gakuwa da ’yar sauraniyar kudancin Kaduna

0
118

Yan bindiga sun yi gakuwa da ’yar Saurauniyar Ikulu a Masarautar Fadar Ikulu da ke Karamar Hukumar Zangon Kataf ta Jihar Kaduna.

Mahara kusan 30 a kan motoci da babura ne suka shiga yankin suna harbi babu kakkautawa, kafin su yi awon gaba da matar, mai suna Benifica Haruna, kafin wayewar garin Talata.

Mahaifiyar gimbiyar, wadda ita ke rike da sarautar Saurauniyar Ikulu, ta bayyana cewa ’yar tata tana daki lokacin aka fara harbe-harben.

“Sai ta kira ni ta ce in samu wuri in boye, ba mu sani ba ashe mu suke nema,” in ji mahaifiyar, wadda ta ce ’yan bindigar sun kusa awa biyu suna cin karensu babu babbaka, jami’an tsaro ba su kawo dauki ba.

Don haka ta bukaci jami’an tsaro su gudanar da bincike domin gano inda ’yar tata take, su kubutar da ita.

Wakilinmu ya kira kakakin ’yan sanda na jihar Kaduna, DSP Muhammed Jalige ko zai samu karin baya, amma har zuwa lokacin da aka kammala wannan labarin babu amsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here