Home Labarai Labaran Duniya Aikin hakar makamin Uranium a Nijar zai fara aiki har zuwa 2040

Aikin hakar makamin Uranium a Nijar zai fara aiki har zuwa 2040

0
115

Ministar dake kulada ma’adinan kasar Hadiza Ousseini ta sanar da kulla yarjejeniyar wadda zata bada damar ci gaba da aiki a mahakar Somair dake yankin arewacin kasar har zuwa Karin shekaru 11 daga yarjejeniyar baya.

Ousseini tace yarjejeniyar ta kunshi bada lasisi da kuma sake fasalin kudinsa a matsayin kamfanin da zai maye gurbin Areva wanda ya kwashe shekaru kusan 50 yana aiki a Nijar domin samarwa Faransa makamashin inganta harkar samar da wutar ta.

Shugaban kamfanin Orano Nicolas Maes yace zasu zuba jarin Dala miliyan 44 a bangaren ilimi da kuma wasu bangarori masu muhimmanci yayin gudanar da ayyukansu a Nijar.

Ministar tace gwamnati da kamfanin Orano sun amince a tsakanin su da su dakatar da aiki a mahakarnijar Imouraren dake samar da tan dubu 200 na uranium har zuwa nan da shekaru 10 masu zuwa.

Jamhuriyar Nijar na daya daga cikin kasashen dake da arzikin uranium da ake amfani da shi wajen gina tashoshin samar da wutar lantarki da kuma gina makamin nukiliya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

X whatsapp