Najeriya ta ce tana aiki da hukumomin da suka jiɓanci yaƙi da fasa-ƙwaurin ɗan’adam don ganin ta kwaso ƴan matan ƙasar da aka kai su yin aikatau a gidajen masu hali na ƙasar Iraƙi.
Ta ce tana fatan yin haka don ganin ta mayar da su gida Najeriya cikin aminci.
Hukumar yaƙi da fasa-ƙwaurin ɗan’adam ta ƙasar (NAPTIP) ta ce tana daɗa shiga damuwa saboda ƙaruwar ‘yan matan Najeriya da ke shiga wahala a Iraƙi.
Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Adekoye Vincent ya fitar ta ambato Babbar Daraktar Naptip tana bijiro da batun a lokacin da take jawabi game da sabbin wurare, da masu fasa-ƙwaurin ɗan’adam ke amfani da su a faɗin duniya wajen safarar ‘yan Najeriya.
A baya dai, ‘yan Najeriya suna zuwa ayyukan ci-rani da aikatau a ƙasashen Gabas ta Tsakiya da na yankin Gulf kamar Saudiyya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, amma ba a saba jin rahotannin kai ‘yan ƙasar zuwa Iraƙi ba.
Sai dai babbar daraktar Naptip, Fatima Waziri-Azi ta ce masu fasa-ƙwaurin ɗan’adam a yanzu sun karkata wajen kai ‘yan Najeriya zuwa Iraƙi don yin aikatau.
A cewarta, ƙoƙari da ayyukan haɗin gwiwa wajen faɗakarwa da hukumarsu ke yi da wasu abokan ƙawance game da illolin fasa-ƙwaurin ɗan’adam zuwa wasu ƙasashe da aka sani, sun sanya masu fasa-ƙwaurin karkata akala zuwa ƙasashe kamar Iraƙi.
Fatima Waziri-Ari ta ce “Matan da aka yi safara zuwa Iraƙi sun cika Naptip da roƙon a kuɓutar da su, kuma a mayar da su gida Najeriya, musamman daga biranen Baghdad da Basra.
Ta ce dillalan ɗaukar aikin sun rarrraba ‘yan matan gida-gida, inda su kuma suka je suka taras da rayuwar ƙasƙanci ta aikatau”.
Hukumar ta ce mafi yawan ‘yan matan Najeriya da ke aiki a Iraqi, ana ci da guminsu ta hanyoyi da yawa, ciki har da tursasa yin lalata da su, abin da ya sa a yanzu suke roƙon a taimaka a mayar da su gida.
Abin na da ban tsoro
Hukumar yaƙi da fataucin ɗan’adam ta Najeriya dai ta ce tana bincike a kan wasu masu ɗaukar aiki ‘yan harƙalla da ke safarar ‘yan matan zuwa ƙasar Iraqi.
Hukumar ta ce bayanan da suka samu na nuna cewa an sha kwantar da ‘yan matan Najeriya masu yawa a asibiti saboda suna aiki na tsawon sa’o’i masu yawa a cikin mawuyacin yanayin da ake tilasta musu.
Kuma da yawa sun yi ƙorafi game da taɓarɓarewar lafiyarsu saboda yawan aiki.
Haka zalika, in ji Naptip ‘yan matan a ko da yaushe suna fuskantar barazanar za a iya cutar da su ko dai kai tsaye daga iyayen gidajensu ko kuma eja-eja ɗinsu na ƙasar Iraƙi, a duk lokacin da suka yi ƙorafi.
“Da yawansu ba su da damar samun wayoyinsu na salula sabida ana ƙwace musu ne nan take da zarar an haɗa su da ubangidan da za su yi wa aiki.