Ɗan bindiga ya buɗewa mutane wuta a Amurka

0
114

Wani dan bindiga a Amurka ya harbe mutum takwas a wajen wani babban kantin sayar da kaya a jihar Texas.

Lamarin ya kai ga kwashe tarin mutane daga wurin, kamar yadda wadanda suka ga lamarin ke bayyana cewa dan bindigar ya rika harbin kan mai-uwa-da-wabi yayin da jama’a ke wucewa.

Mutumin ya kai harin ne a kantin da ake kira Allen Premium Outlets a lokacin ana tsakar hada-hadar sayayya.

Wurin na da nisan kusan mil talatin ne daga Dallas.

Hukumar ‘yan sanda ta ce akwai wani jami’inta da ke yankin a lokacin ko da yake ba yaje ba ne domin wannan lamari.

Ta ce jami’in ya kasance ne a yankin domin wani kira na daban, sai kawai aka yi gamo da katar ya ji karar harbin, nan da nan ya garzaya ya kuma taki sa’a ya kashe dan bindigar.

Hukumar ‘yan sanda ta ce akwai wani jami’inta da ke yankin a lokacin ko da yake ba yaje ba ne domin wannan lamari.

Ta ce jami’in ya kasance ne a yankin domin wani kira na daban, sai kawai aka yi gamo da katar ya ji karar harbin, nan da nan ya garzaya ya kuma taki sa’a ya kashe dan bindigar.

Hukumomi sun ce suna ganin dan bindiga-dadin ya yi wannan aika-aika ne shi kadai ba da hannun kowa ba.

Mutum shida ne suka mutu nan take yayin da wasu biyu da aka garzaya da su asibiti suka cika a can.

Akwai kuma wasu uku da suke cikin mawuyacin hali, yayin da wasu hudu da lamarin ya rutsa da su ke samun sauki.

Yawancin wadanda abin ya shafa yara ne.

Binciken da wata kungiya ta yi a kan irin wadannan harbe-harbe na tarin jama’a na ba gaira ba dalili a Amurka, ta gano cewa zuwa yanzu an yi irinsa 199 a shekarar nan kadai.

Gwamnan jihar Texas Greg Abbott ya bayyana harin a matsayin mummunan abin takaici.

Sannan ya ce a shirye jihar take ta taimaka wa hukumomin yankin.

Hukumar ‘yan sandan Amurka ta bukaci jama’a da suka dauki hoton bidiyo na abin da ya faru da su tuntubi hukumar binciken manyan laifuka ta kasar, FBI, wadda ke tattara sheda.

Yawancin mutane a jihar ta Texas da suka kai shekara 21 zuwa sama suna da damar rike bindiga ba tare da lasisi ba, sai dai idan an taba kama su da laifi a kotu.

Sannan kuma dokokin mallakar bindigogi a jihar ‘yan kadan ne kawai.

A farkon makon nan ‘yan sanda a jihar ta Texas suka kama wani mutum da ake zarginsa da harbe makwabtansa mutum biyar ciki har da yaro mai shekara tara

An kama Francisco Oropesa ne yana boye a cikin wani kwabet bayan kwana hudu ana farautarsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here