APC ta nuna goyon baya ga Sen Akpabio don shugabancin majalisa ta 10

0
115

Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, ta amince da rabon mukamai na shugabancin majalisa ta goma.

Ta ce ta amince da Sanata Godswill Akpabio a matsayin shugaban majalisar dattijai daga shiyyar Kudu maso Kudu.

Haka zalika, Sanata Barau Jibrin zai kasance mataimakin shugaban majalisar dattijai daga Arewa maso Yamma.

Wata sanarwa da jam’iyyar mai mulki ta fitar, ta ambato kwamitin gudanarwa na APC yana cewa matakin ya zo ne bayan rahotannin tuntuba da tarukan da jam’iyyar ta yi da zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.

Da kuma shugabannin jam’iyya da sauran masu ruwa da tsaki game da rabon mukamai zuwa shiyyoyi daban-daban na kasar game da jagorancin majalisa ta goma

A Majalisar Wakilai kuma, APC ta ce tana goyon bayan Hon Abbas Tajuddeen a matsayin shugaban majalisar ta wakilai daga Arewa maso Yamma.

Sai Ben Kalu a matsayin mataimakin shugaban majalisar wakilai daga Kudu maso Gabas.

Sanarwar ta ce Kwamitin Gudanarwar APC na Kasa ya lura cikin mutuntawa da sakamakon taruka tsakanin zababben shugaban kasa da shugabancin kwamitin.

Wannan mataki ya tabbatar da rade-radin da aka dade ana yi cewa APC ta bai wa Sanata Godswill Akpabio matsayin shugaban majalisar dattijai da kuma Abbas Tajuddeen matsayin shugaban majalisar wakilai da za a bude a nan gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here