‘Yan bindiga sun sace ‘ya’ya da jikokin Sarkin Kagarko a fadarsa

0
99

‘Yan bindiga sun dirar wa fadar Maai Martaba Sarkin Kagarko, Alhaji Sa’ad Abubakar da ke jihar Kaduna ta Najeriya, inda suka yi awon gaba da ‘ya’yansa guda 9 da suka hada da jikokinsa da kuma wasu mutanen daban.

Rahotanni na cewa, ‘yan bindigar sun kuma sace amaryar sarkin wadda daga bisani ta kubuta daga hannunsu tare da komawa gida kamar yadda wadanda suka shaida lamarin suka bayyana.

Wadanda suka shaida lamarin sun bayyana cewa, ‘yan bindigar sun kai farmaki ne da misalin karfe 11 da minti 15 na safiyar wannan rana ta Litinin.

An kuma ce, ‘yan ta’addar sun kashe wani makiyayi a kauyen Kuchimi, sannan suka wawure kayayyakin akalla shaguna bakwai a kauyen Janjala a Karamar Hukumar  Kagarko a yayin komawa tungarsu.

Kawo yanzu rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ba ta ce komai ba game da sabon farmakin.

Jihar Kaduna na daya daga cikin joihohin arewacin Najeriya da suka fi fama da hare-haren ‘yan bindiga wadanda har yanzu hukumomi suka gaza kakkabe su baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here