Manoman tumatir a jihar Kano da ke Najeriya sun tafka asarar sama da Naira biliyan 1 da biliyan 500 kuma har yanzu suna ci gaba da kidayar asarar wadda wata shu’umar tsutsa ta haddasa musu.
Tsutsar da ake kira ‘Tuta Absaluta’ ta lalata gonakan tumatiri da dama, lamarin da ya durkusar da manoman sama da dubu biyar a jihar.
Wannan ibtila’in ya haifar da karancin tumatur a sassan jihar Kano da kewaye.