Jami’an rundunar Ƴan sandan Najeriya dake jihar Katsina sun samu nasarar harbin wani mai ƙwacen waya salula a kafar sa tare da kama shi a jihar Katsina.
Kamar yadda kakakin rundunar Ƴan sandan, CSP Gambo Isah ya bayyana, wanda jami’an yan sandan suka harba sunan sa Nasiru Babangida wanda aka fi sani da Ɗan Ruma.
Gambo Isah ya cigaba da cewa wannan ya biyo bayan umurnin da Kwamishinan Ƴan Sandan jihar ta Katsina ya bayar ga jami’an su cewa su harbe duk wanda suka samu da laifin ƙwacen waya da kuma ƙauranci a jihar.
Haka zalika rundunar ta ƴan sanda ta kuma kama wasu yan daba su kimanin sama da 70 da laifin yawo da makami da kuma tada hatsaniya a sassa daban daban na jihar ta Katsina.
Daga karshe dai CSP Gambo Isah ya bayar da tabbacin cewa jami’an su za su cigaba da bi lungu da sako na jihar suna kamo ƙauraye har sai sun tuba sun dena.