Buhari na shirin ciyo bashin Dala miliyan 800

0
110

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci Majalisar Dattawan kasar da ta amince masa ciyo bashin Dala miliyan 800.

Shugaba Buhari ya gabatar da bukatar ce a cikin wata wasika da ya shugaban majalisar, Ahmad Lawan ya karanta a wani zama da mambobin majalisar suka yi a jiya Talata.

A cikin wasikar, shugaba Buhari ya yi bayanin cewa, za a yi amfani da bashin ne domin fadada wani shiri na samar da walwalar jama’ar musamman talakawa da gajiyayyu a fadin kasar.

Shugaba Buhari ya ce, za a ciyo sabon bashin ne daga Bankin Duniya.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban ke shirin mika mulki a ranar 29 ga wannan wata na Mayu ga magajinsa, Bola Ahmed Tinubu da ya lashe zaben shugaban kasa a cikin watan Fabairun da ya gabata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here