Hatsarin mota ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 20 a jihar Katsina

0
125

A daren ranar Lahadi 7/05/2023 wani hatsarin Mota ya afku akan hanyar Malumfashi dai dai Ƙwanar Gora inda yayi sanadiyyar Mutuwar aƙalla Mutane 20 tare da jikkata mutane da dama waɗanda yanzu haka suna babban Asibitin Garin Malumfashi wato Asibitin ƙwandala suna karɓar kulawar Likitoci.

Ita dai wannan motar tirela ɗauke da shanu da mutane tayi mummunan hatsari a kwanar Garin Gora dake a ƙaramar hukumar Malumfashi a jihar Katsina inda mutum 20 a ciki suka rasa rayukansu a daren jiya Lahadi.

Motar dai ta taso ne daga ƙaramar hukumar Charanchi da niyyar zuwa Garin Benin dake jihar Edo.

A cewar ɗan uwan wasu daga cikin waɗanda suka rasu, mamatan cewa sun taso ne ajiya da daddare da zummar zuwa jihar Edo yayinda suka zo ƙwanar Gora kan motar ya tsinke ya fita daban ya rabu da sauran jikin Motar.

Baya ga mutum aƙalla 20 da suka rasu, wasu da dama sun jikkata kuma yanzu haka suna cigaba da karbar magani a babbar asibitin garin Malumfashi

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here