An bude kasuwar da aka rufe saboda kazanta a Abuja

0
116

Hukumar Birnin Tarayya ta sake bude Kasuwar Garki wadda ta rufe saboda rashin kula da tsaftar muhalli.

Hukumar ta bude kasuwar ne bayan kwana shida da rufe ta saboda matsalar kazantar.

Amma a yammacin ranar Laraba, babban mashawarcin Ministan Birnin Tarayya a bangaren sanya ido da tabbatar da bin doka, Ikharo Attah, ya ba da izinin bude kasuwar ta Garki, bayan ’yan kasuwar sun cika ka’idojin da aka shimfida na tsaftar muhalli.

Attah ya bayyana gamusarsa da yadda ’yan kasuwar da shugabanninsu suka gaggauta daukar mataki domin tabbatar da tsafta.

Amma ya gargade su da cewa hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen sake rufe kasuwar, idan ’yan kasuwar suka sake sakaci da batun na tsaftar muhalli.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here