Mene ne zakami, wanda shayinsa ya halaka wasu matasa a Kano?

0
119

Daya daga cikin labaran da suka fi jan hankalin jama’a a birnin Kano da ke arewacin Nijeriya a wannan mako shi ne yadda ake zargi wani shayi da aka hada da zakami ya yi sanadin mutuwar wasu matasa yayin bikin auren abokinsu.

Bayan wadanda suka rasu, an kwantar da wasu daga matasan da suka sha zakamin a asibiti.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, SP Haruna Kiyawa ya ce sun fara bincike kan al’amarin kuma za su yi bayani ga manema labarai da zarar sun kammala shi.

Akwai shayi iri-iri da ake dafawa da suka shahara ba ma a Nijeriya kawai ba, har da duniya baki daya.

Daga cikin dangogin shayin da suka yi suna sosai a arewacin Nijeriya akwai Shayin Zakami da Shayin Gadagi da Shayin Goruba da Shayin Kayan Kamshi da sauran su.

Sai dai galibi ana shan shayin zakami da shayin Gadagi ne don kara kuzari, kamar yadda masu tu’ammali da su ke cewa.

Wannan rubutu zai yi nazari ne a kan ma’anar shayin zakami a gargajiyance da kuma a likitance.

Mene ne Zakami a “gargajiyance”?

Akan dafa itaciyar a sha a matsayin shayi wanda kan sa a bugu. Hoto/Getty Images

Wasu masu shayi biyu a jihar Kano da TRT Afrika ta zanta da su wadanda suka bukaci a boye sunayensu, sun ce zakami wata itaciya ce da take fitowa a gefen ruwa.

“Itaciyar zakami tana kama da ‘ya’yan auduga. Akan debi ‘ya’yan a dafa kamar shayi a dinga sha.

“Kuma mutane suna sha ne don su bugu,” kamar yadda daya daga cikin masu shayin ya shaida wa TRT Afrika.

Zakami a ma’aunin kimiyya

A hirarsa da TRT Afrika, Dokta Amiru Yola, wani kwararren likita a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano, ya ce zakami wani itace ne da ke fitowa a wani yanayi na shekara, kuma yake bushewa ya mutu, sai ‘ya’yansa su shiga cikin kasa.

Idan damina ta zo sai ya sake fitowa, a takaice dai kamar ciyawa yake.

Sunan zakami da Turanci ko kimiyya “Datura Ballerina ko Datura Metel ko Devil’s Trumpet,” a cewar Dokta Amiru.

Gaba daya karan zakamin ba ya wuce mita daya, amma yana da ‘ya’ya da ganye da jiki da kuma tushe kamar yadda likitan ya bayyana.

“Kuma a duk jikin nasa za a iya samun sinadarin zakamin da ake amfani da shi wajen sa wa a shayi ko a tauna ko a sa a abinci,” ya ce.

Mene ne amfanin zakami?

Dokta Yola ya bayyana cewa a likitance zakami yana da amfani, don ana amfani da shi wajen harhada wasu magunguna.

Ya kuma ce dalilin da ya sa mutane ke bibiyarsa don yin wani abu da shi daban ba zai rasa nasaba da fahimtar da suka yi ta yadda yake da amfani a jikin dan adam ba.

“Ana hada magunguna kamar su Atrophine mai sinadarin Hyoscine, wanda shi kuma ana samun sa ne a cikin zakamin,” in ji likitan.

Akan yi amfani da zakami ta wurare da yawa kamar samar da maganin asibiti na rage radadi ko zafin zazzabi ko matsalar ciwon zuciya.

Sannan ana sarrafa shi ta wajen hada magungunan samun haihuwa, ko maganin magance matsalar rashin barci ko magungunan rage tashin hankali da damuwa.

Kazalika likitan ya ce ana sarrafa shi wajen hada maganin fito da gashin kai.

Illolin zakami

Ba likita kawai ba, hatta masu shayin da TRT Afrika ta yi hira da su sun bayyana cewa shan Zakami ba bisa ka’ida ba yana da hadari da illa sosai.

Dokta Yola ya ce babban abin al’ajabin shi ne yadda har mutane suka gano yana sa kuzari da kaurantaka da sauran su.

Wani mai shayi ya ce yawanci masu tu’ammali da kwayoyi na hadawa da Zakami ne don yana kara musu rashin tsoro da jajircewa.

Sai dai Dokta Yola ya ce idan zakami ya yi yawa yana jawo rashin kuzari da rashin karfi da rage gudun bugun zuciya da zafin jiki da kuma mummunan zazzabbi.

“Idan mutum ya sha ba bisa ka’ida ba ko ya sha da yawa, kan ka ce mene ne wannan sai mutum ya hau kyarma yana neman fizgo iska don shaka.

“Idan bai samu taimakon gaggawa ba sai mutum ya mutu nan da nan,” ya ce.

Likitan ya jan kunnen ma’abota shan zakami sosai da cewa su guji tu’ammali da itacen don ba sa sha bisa tsari kuma ba tare da an sarrafa shi ba, lamarin da ka iya yi musu mummunar illa.

Ya ce wannan lamari na mutuwar matasa ba shi ne karo na farko da zakami ya jawo asarar rayuka ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here