Za a dauki mataki kan kwamandan FRSC mai son aiki da Shari’ar Musulunci a Najeriya

0
106

Hukumar kiyaye hadarurruka ta Nijeriya, FRSC, ta ce za ta dauki mataki kan kwamandanta na Bauchi kan wasu kalamai da ya yi da hukumar ta ce sun saba wa dokar aikin hukumar.

Jaridun Nijeriya kasar sun ambato kwamandan na Bauchi yana cewa zai soma aiki da Shari’ar Musulunci wurin hukunta wadanda suka saba dokar hanya domin rage aukuwar hadarurruka.

Ya ce dokokin da ake amfani da su yanzu ba su da tsauri shi ya sa mutane ke jawo hadarurruka yana mai shan alwashin amfani da Shari’ar Musulunci domin taimaka wa wurin kiyaye hadarurruka.

Sai dai a sanarwar da hukumar ta FRSC ta fitar a ranar Asabar, ta nesanta kanta da kalaman kwamandan inda ta ce ra’ayinsa kawai ya fada.

“Akwai bukatar jama’a su sani cewa kalamansa baki daya ba su da alaka da matsayar hukumar kiyaye hadarurruka ta kasa.

“Nan take shugaban hukumar Dauda Ali Biu ya bukaci kwamandan ya dawo hedikwata Abuja domin a dauki matakan da suka dace a kansa saboda kalamansa sun saba wa ka’idar aikin FRSC,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta jaddada cewa FRSC ba hukuma ce ta addini ko bangaranci ba tana mai karawa da cewa hukuma ce ta Gwamnatin Tarayyar Nijeriya da aka kafa ta kan kundin tsarin mulki ba shari’a ba.

Ana yawan samun hadarurrukan ababen hawa a Nijeriya lamarin da ke sanadiyyar mutuwar mutane da dama a duk shekara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here