Maki uku Man City ke bukata ta lashe Premier League

0
82

Manchester City na bukatar cin wasa daya nan gaba ta lashe Premier League, bayan da ta doke Everton 3-0 a wasan mako na 36 ranar Lahadi.

Minti na 37 da take leda Ilkay Gundogan ya ci kwallo, kuma minti biyu tsakani Erling Haaland ya kara na biyu, kuma Gundogan ne ya saka masa tamaular.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Gundogan ya kara na uku na biyu da ya zura a raga a karawar ta Goodison Park.

Karo na biyu kenan da Gundogan ya zura biyu a raga ya kuma bayar aka ci a Premier tun bayan Oktoban 2016 a fafatawa da West Brom.

Kungiyar da Pep Guardiola ke jan ragama na neman maki uku a karawa ukun da ya rage mata da za ta yi da Chelsea da Brighton da kuma Brentford.

Rashin nasara da Everton ta yi ya sa ta koma ta 17 da tazarar maki daya tsakaninta da Leeds, wadda take ‘yan ukun karshen teburi.

City ta samu wannan damar bayan da Brighton ta je ta doke Arsenal 3-0 ranar Lahadi a karawar mako na 36 da suka fafata.

Saura wasa biyu ya rage wwa Arsenal, wadda take da maki 81, koda za ta lashe su za ta hada maki 87, yayin da City tana da 85, wadda take da karawa uku a nan gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here