An binne mutanen da suka mutu a harin Mangu cikin ƙaton kabari’

0
85

Mutane da dama sun tsere bayan wani hari da aka kai kan ata al’umma da ya haddasa mutuwar gommai sannan aka binne wasu a wani wawakeken kabari.

Mazauna Mwaghavul, al’ummar da ta yi fice a harkar noma a ƙaramar hukumar Mangu sun shaida wa BBC cewa maharan sun kutsa cikin ƙauyukansu ranar Talata inda suka buɗe wuta kan mutane tare da cinna wa gine-gine wuta.

Deborah Samuel ta ji ƙarar bindiga yayin da take cikin kasuwa inda kuma ta yi ta kanta.

Ta ce an kashe sirikinta da ƙannen mijinta su huɗu.

“Mun soma jin ƙarar harbe-harbe ta ko ina. Sai muka fara gudu. Har yanzu ina jin ciwon abin da ya faru,” Deborah ta bayyana hakan yayin da take riƙe da jaririnta ɗan watanni.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Plateau Alabo Alfred ya ce ba zai iya bayar da bayani ba kan lamarin saboda ana ci gaba da gudanar da bincike.

Sai dai ya ce shugaban ƙungiyar ci gaban al’ummar yankin, Joseph Gankat, ya ce adadin mutanen da suka mutu sun kai 85 kuma ana ci gaba da neman mutanen da suka yi ɓatan dabo.

Ya ƙara da cewa “ƴan bindigar sun kai samame a kusan ƙauyuka 17”.

Shugaban al’ummar Fulani a yankin, Adamu Usman shi ma ya faɗa wa BBC cewa mutum 30 cikin al’ummar yankinsa aka kashe.

Jesse Jwanle, wani rabaran a wani coci da ke ƙauyen Gaude ya ce an kashe ɗaya daga cikin mambobin majami’arsa, an ƙona gidansa da cocin.

“Sun soma ƙona gidaje. Duka dukiyata da ke gidan ta ƙone ban da kayan da ke jikina. Na rasa abubuwa da dama a gida,” in ji Jesse.

Mutane da dama kamarsa sun tsere. Wasu kuma sun nemi mafaka a wani sansani da ba na gwamnati ba.

An binne mutanen da suka mutu a wani ƙaton kabari, in ji jagororin al’ummar.

Babu masaniya kan abin da ya janyo harin amma wasu mazauna yankin sun ce ya yi kama da harin ramuwar gayya kan wani hari da aka kai wa al’ummar Fulani cikin watannin da suka gabata.

Gwamnatin jihar ta nemi jama’a su kwantar da hankalinsu inda ta yi alƙawarin kai kayan agaji ga mutanen da lamarin ya shafa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here