Hukumar FA ta yi wa Jurgen Klopp na Liverpool dakatarwar wasanni 2

0
117

Wannan dakatarwa dai na nuna cewa, Bajamushen mai horarwar zai rasa damar sanya ido kan tawagarsa a wasan da za su karbi bakoncin Aston Villa ranar lahadi mai zuwa a filin wasa na Anfield.

Baya ga haramcin wasannin biyu Klopp zai kuma biya tarar fam dubu 75.

Yayin wasan dai Jurgen Klopp kamar yadda ya saba ya yi wani salon murna bayan kwallon mintina 94 da ta basu gagarumar nasara kan Tottenham inda a cewarsa, alkalin wasa Tierney y ace massa bai dace ba tare da bashi jan kati.

Wannan mataki ya sanya Klopp tambayar Tierney ko ya na da wani kulli game da Liverpool? Kalaman da aka bayyana a matsayin wadanda basu dace su fita daga bakin mai horarwar ba.

Hukumar da ke kula da alkalan wasannin dai ta yi watsi da zargin da Liverpool ta yi kan cewa Tieney na da kulli akan kungiyar hatta bayan aike mata takardar korafi kan zarge-zargen da suke da shi kan alkalin wasan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here