Home Labarai Saudiya tayi nasarar raba wasu tagwayen Najeriya da aka haifa a manne...

Saudiya tayi nasarar raba wasu tagwayen Najeriya da aka haifa a manne da juna

0
134

Rahotanni sun ce jiya alhamis aka gudanar da aikin a asibitin yara na Sarki Abdallah, kuma ya kunshi likitoci 35 da kwararru akan aikin kula da lafiya da kuma masu taimakawa likita.

Shugaban kula da Cibiyar kula da ayyukan jinkai na Sarki Salman wanda shine ya jagoranci likitocin da suka gudanar da aikin, Abdullah bin Abdulaziz al-Rabeeah yace sakamakon nasarar da aka samu na raba tagwayen biyu, an fara aikin sake fasalin bangarorin da aka raba a jikinsu.

Su dai wadannan tagwaye an haife su ne a asibitin koyarwar Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariaa watan janairun bara, inda suka manne da juna a cibiya da hanta da hanji da mafitsara da mahaifa da kuma kasusuwan kugu.

Bayan haihuwar su an kai su asibitin kasa na Abuja amma suka kwashe watanni 8 ba tare da an musu aiki ba saboda rashin kudi, abinda ya sa gwamnatin Saudi Arabia ta dauki nauyin musu aikin kyauta.

Su dai jariran biyu Hassana da Hussaina sun isa Saudi Arabia ne ranar 8 ga watan Disambar bara vayan daukar su da jirgin saman da ake daukar marasa lafiya.

Wannan dai shine karo na 56 da Cibiyar jinkai ta Saudi Arabia ta gudanar da wannan aiki a cikin shekaru 33.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

X whatsapp