Edouard Mendy zai maye gurbin Hugo Lloris, Harry Maguire na duba yiwuwar barin Manchester United

0
90

Tottenham na Shirin yin bazata wajen dauko mai tsaron gidan Chelsea da Senegal Edouard Mendy, mai shekara 31, don maye gurbi Hugo Lloris mai shekara 36, bayan kammala kwantiragin sa da kungiyar. (Sun)

Dan wasan Manchester United da Ingila, Harry Maguire, na duba yiwuwar barin kungiyar ya koma West Ham, bayan da dangartakar sa da Erik ten Hag, ta yi tsami. (Football Transfers)

Mai horas da ‘yan was an kungiyar Chelsea da ke rikon kwarya Frank Lampard, ya ce a baya a lokacin da yake kungiyar ya yi yunkurin dauko dan wasan Norway da Manchester City Erling Haaland mai shekara 22 zuwa Chelsea kafin komawar sa Borussia Dortmund. (Mail)

Tottennhan na kan gaba wajen bukatar dauko mai horas da Feyenoord Arne Slot a matsayi manajan kungiyar, a yayin da kungiyarsa ta Feyenoord ke dari-darin tafiyar sa Ingila. (Sky Sports)

Rahotanni sun ce dan wasan tsakiya na Chelsea da Ingila Ruben Loftus-Cheek mai shekara 27, na azarbabin koma wa AC Milan, tun da AC Milan din ta nuna sha’awar daukarsa. (Fabrizio Romano)

Tun bayan sanarwar barinsa Manchester United, dan was an bayan kungiyar, Phil Jones, dan shekara 31, ke tunanin inda zai koma buga tamaula a kakar wasanni mai zuwa. (Lancashire Telegraph)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here