Wata mata ta auri kanta a Amurka

0
107

Wata mata a ƙasar Amurka mai suna Dorothy Fedeli, ta auri kanta shekara 50 bayan mutuwar aurenta.

Matar ta ce “Na iya ƙoƙarina amma na kasa, to me ya sa ba zan auri kaina ba?” Kamar yadda ta faɗa kafin sanar da auren.

Dorothy Fedeli, mai shekaru 77, ta auri kanta ne a wani bikin iyali da aka yi jihar Ohio na Amurka.

Wani abin mamaki shi ne amaryar ta yi aure shekaru 50 da suka gabata, kuma bayan rabuwar auren ne, ta sha alwashin ba za ta ƙara aure ba.

Dorothy dai na da ‘ya’ya uku da kuma jika ɗaya.

An ga matar sanye da fararen kaya tare da riƙe furanni a hannunta.

Ɗaurin auren ya samu halartar ƴan uwa da kuma abokai.

Ta ce ra’ayin auren kanta ya zo mata a lokacin da take cikin coci. Ta shaida wa “Today.com” cewa ta shafe shekaru 40 tana zama ita kaɗai, kuma ta yanke shawarar yin wani abu na musamman da kanta.

Fedeli ta ce tana cike da annashuwa kamar kowace amarya a ranar aurenta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here