Ba zan daina rusau da korar ma’aikata ba, har na bar mulki – El-Rufai

0
116

Gwamnan Kaduna mai barin gado, Nasir El-Rufai, ya ce ba zai daina da korar bara-gurbin ma’aikata da rusa haramtattun gine-gine ba, har sai ya bar mulkin jihar.

El-Rufai ya yi wannan faruci ne washegarin da ya kwace izinin mallaka tare da sanya alamar rusa wasu kadarori tara mallakin tsohon gwamnan jihar, Sanata Ahmed Mohammed Makarfi.

Da yake bayani a taron kaddamar da littafin da wani dan jarida, Emmanuel Ado, ya rubuta a kan ayyukansa, mai suna “Putting The People First”, ya ce, “Har zuwa ranar karshen mulkina, ba zan daina kawar da bara gurbin mutane da sauran miyagun abubuwa ba.”

A cewarsa, “Duk abin da na ga bai dace ba, zan kawar da shi, saboda kada su zama matsala ga sabon gwamnan da zai karbi mulki.”

A lokacin taron, Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya bayyana El-Rufai a matsayin mutum mara tsoro, wanda samun mai tsage wa gwamnati gaskiya kamarsa, ke da wuya.

A cewar Wike, “Samun shugaba irin El-Rufai sai an tona, wajen hazaka da jarumta domin tabbatar da adalci ga kowa.

“Shi ba dan amshin shata ba; Ba zan manta wasikarsa ga Shugaba Buhari a watan Maris na 2017 ba, wanda ya tayar da kura, inda ya ja hankalin shugaban kasa kan muhimmancin cika alkawuran da ya yi wa jama’a saboda kada ya bar mummunan tarihi.

“Da wuya a samu gwamnan da zai iya yin haka ga shugaban dan jam’iyyarsa, in ba jarumi wanda ba dan kanzagi ba.”

A wurin taron, Wike ya ba da gudummawar Naira miliyan 20, haka ma shugaban kasa mai jiran gado, Bola Ahmed Tinubu, wanda tsohon Shugaban Asusun Kula da Manyan Makarantu ta Kasa (TETFUND), Kashim Imam, ya wakilta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here