Chelsea ta taya Vlahovic, Barca za ta dauki Neves na Wolves

0
91

Chelsea ta taya dan kwallon Juventus, Dusan Vlahovic, mai shekara 23, kan fan miliyan 70, domin ta dauka a karshen kakar nan. (ESPN)

Itama Manchester United na fatan sayen Vlahovic, wanda ya fayyace cewar yana kwadayin buga Champions league a badi. (Football Transfers)

Leicester City na shirin tuntubar tsohon kociyan Brighton da Chelsea, Graham Potter kan bashi aikin jan ragamar kungiyar a badi. (Football Insider)

Kociyan Roma, Jose Mourinho na son daukar Youri Tielemans, wanda yarjejeniyarsa a Leicester City za ta kare a karshen kakar nan. (Gazzetta dello Sport – in Italian)

Barcelona ta kulla yarjejeniya da eja din ‘yan kwallo kan daukar dan wasan Wolverhampton, Ruben Neves, wanda ake sa ran za a yi musaya da Ansu Fati a kunshin kwantiragin. (Sport – in Spanish)

Aston Villa na duba ko za ta iya daukar aron dan wasan Manchester United, Anthony Martial a karshen kakar nan. (Football Transfers

Crystal Palace na son yin zawarcin dan kwallon Bournemouth, Jefferson Lerma, wanda kwantiraginsa zai karkare a kungiyar da zarar an kammala kakar bana. (Sun)

Nottingham Forest na fatan mallakar Golan Manchester United, Dean Henderson, wanda ke wasannin aro a kungiyar a bana. (Telegraph – subscription required)

Manchester United na tattaunawa da Facundo Pellistri kan mika masa kunshin kwantiragi da zai ci gaba da taka leda a Old Trafford zuwa Yunin 2028. (Fabrizio Romano)

A shirye Manchester City take ta sayar da mai tsaron raga Zack Steffen idan yarjejeniyar da yake buga wa Middlesbrough wasannin aro ta cika. (Sun)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here