Najeriya da Liberia da taimakon Amurka za su yi kawancen yaki da ta’addanci

0
112

Hafsoshin tsaron kasashen Najeriya da Liberia da taimakon Amurka sun sha alwashin hada hannu don aiki tare, da kuma musayar dabaru a kokarin kawo karshen matsalolin tsaron da suka dabaibaye su.

Kasashen yayin babban taron tsaro na shekara shekara da ya gudana a Ivory Coast cikin makon jiya, wanda Ofishin Amurka kan sha’anin nahiyar Afrika AFRICOM ya dauki nauyi a wannan karon, ya mayar da hankali game da hadakar da za ta kai ga nasarar murkushe barazanar ta’addanci tsakanin kasashen na Afrika.

Babban kwamandan Sojin Najeriya Manjo Janar Christopher Musa da ya wakilci kasar a wajen taron wanda ya hado manyan hafsoshin sojin kasa daga kasashe daban-daban, ya ce har sai kasashe sun hada hannu ne za a iya samun gagarumar nasarar murkushe barazanar ta’addanci.

AFRICOM ya bayyana cewa har kullum Amurka a shirye ta ke ta yi hadin gwiwa da kasashen na Afrika wajen samar da cikakken tsaro a nahiyar tare da murkushe barazanar ayyukan ta’addanci.

Taron na bana dai na zuwa ne a dai dai lokacin da ake ganin raguwar ayyukan ta’addancin kungiyoyin Boko Haram da ISWAP da akalla kashi 15 tun daga shekarar 2020 idan aka kwatanta da alkaluman 2019, duk da cewa alkaluman kungiyar da ke tattara hare-haren ta’addanci ta Global Terrorism Trends na nuna cewa har yanzu kungiyoyin ke aikata kashi 8 na ayyukan ta’addanci a Duniya.

Baya ga Najeriya kasashe irin su Kamaru da Chadi da kuma Nijar dukkaninsu na ganin hare-haren kungiyoyin na Boko Haram da ISWAP, ko da ya ke jami’an tsaro na gagarumar nasara akansu a baya-bayan nan.

Taron na bana da Ivory Coast ta karbi bakonci a birnin Abidjan baya ga kwamandojin sojin kasahen Afrika 39 da suka halarci taron akwai takwarorinsu kwamandojin soji daga kasashen Amurka da Brazil baya ga wakilci daga soji da dukkanin kasashen Turai 46.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here